N40 Ake Biya: Matashi Ya Bayyana Rasit Din Kudin Makarantarsa na 1994

N40 Ake Biya: Matashi Ya Bayyana Rasit Din Kudin Makarantarsa na 1994

  • Wani mutumi 'dan Najeriya, Sir Jarus, a dandalin Twitter ya dora gami da bayyana irin arhar da kudin makarantar da yayi karatu yayin da yake tasawa
  • A wallafarsa, ya bayyana yadda ya biya N40 a JSS 1 a 1994 da kuma N1,090 na komai da ya shafi karatunsa duk da hayar daki a jami'a a 2001
  • A cewarsa, jimillar kudin da ya kashe a ilimin Boko daga firamare zuwa jami'a bai kai N200,000 ba

Wani mutumi 'dan Najeriya mai suna Sir Jarus ya bayyana kididdigar kudin da ya kashe na gaba daya rayuwar makarantarsa a matsayinsa na dalibi.

Kamar yadda ya bayyana, ya biya N40 a matsayin kudin makaranta yayin da yake ajin farko a sakandiri (JSS 1) a shekarar 1994.

Kudin Makaranta
N40 Ake Biya: Matashi Ya Bayyana Rasit Din Kudin Makarantarsa na 1994. Hoto daga @sirjarus/TikTok
Asali: UGC

Bayan ya samu gurbin karatu a Jami'ar Obefemi Awolowo, ya biya kudi N1,090 a shekararsa ta farko a jami'a (100 level) a matsayin kudin da ya kunsa duk wani abu da ya shafi karatu da kuma matsugunni a shekarar 2001.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaban Kasa Ya Tsira Daga Yunkurin Tsige Shi a Majalisar Dattawa – Sanatan PDP

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da bayyana yadda ya kashe kimanin N15,000 a shekararsa ta karshe a jami'a. Jarus ya ce gaba daya kudin da ya kashe daga matakin firamare zuwa sakandiri bai kai N200,000.

Kamar yadda ya rubuta:

"Kudin makarantar zango na daya a shekarata ta farko a sakandiri N40 (Naira arba'in) a 1994. Na biya N1,090 (Dubu daya da naira cassa'in) a matsayin kudin makaranta da matsugunni a shekarar 2001.
"Na biya 15,000 ko kusan haka a shekarata ta karshe. Gaba daya jimillar kudin da na kashe a ilimin Boko na daga matakin firamare zuwa kammala jami'an bai kai N200,000."

Martanin 'yan soshiyal mediya

@sharperleinado ya ce:

"Najeriya tayi kokari kuma tana cigaba da kokarin da da yawa daga cikinmu. Dukkanmu mun amfana ta wani wurin ko wani gurin."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu Ya Bincika Tarihin Peter Obi, Ya Nada Masa Sabon Suna

@VOluwayemi yayi tsokaci:

"Nayi imani duk da irin arhar da kayi karatu hakan ba yana nufin iyayenka sun biya kudin makarantarka cikin sauki ba a lokacin ku a makaranta. Gaba daya karatun da nayi a Ìfe bai kai N50,000 ba nima.
"Ilimi kyauta ne a makarantar gwamnati, a firamare na da sakandiri."

@KalimatSuleiman ya kara da cewa:

"Yanzu suna son kwace wannan damar daga daliban Najeriya tare da 'janyo tsadar ilimi' - kamar bashi ga dalibai bayan kara kudin makaranta yadda da yawa ba za a iya biya ba gami da datse tallafin a ilimin makarantar gaba da sakandiri."

@yemileel ya ce:

"Gaskiya tayi matukar arha yallabai."

@segun_are ya ce:

"Ilimi ba zamba bane. Ka narka kasa da N200,000 amma kana girbar daruruwan bandira."

Rasit ya nuna Dantata yana cikin 'yan Najeriya na farko da suka fara zuba kudi a banki

A wani labari na daban, wani tsohon rasit da ya bayyana a Twitter ya nuna yadda Alhaji Alhassan Dantata ya zama cikin 'yan Najeriya na farko da suka fara zuba kudadensu a banki.

A wancan lokacin, bankin Turawa ne aka bude wanda yanzu shi ake kira da First Bank.

Asali: Legit.ng

Online view pixel