Jerin Gine-Gine 7 Da Shugaba Buhari Ya Kaddamar A Yobe Jiya

Jerin Gine-Gine 7 Da Shugaba Buhari Ya Kaddamar A Yobe Jiya

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 9 ga watan Junairu 2023 ya kai ziyara jihar Yobe domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da aka kammala.

Buhari ya shiga Damaturu ne daga jihar Adamawa bayan halartan taron kamfen kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Shugaban kasan ya samu kyakkyawan tarba daga wajen gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni; Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan; tsohon gwamnan Yobe, Ibrahim Geidam da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum.

Buhari
Jerin Gine-Gine 7 Da Shugaba Buhari Ya Kaddamar A Yobe Jiya
Asali: Twitter

Kalli jerin ayyukan da Shugaba Buhari ya kaddamar:

  1. Tashar Jirgin Saman Saukan Kayayyakin Na Kasa da Kasa
  2. Kasuwar Damaturu
  3. Sashen kula da yara da mata na asibitin koyarwan jami'ar jihar Yobe
  4. Rukunin gidaje dake Potiskum
  5. Babbar makarantar Damaturu
  6. Sabuwar ofishin yan sanda HQ
  7. Asibitin Yan Sanda

Kara karanta wannan

2023: Dalilin 1 Da Yasa Har Yanzu Bamu Bayyana Wanda Muke Goyon Baya Ba: Dattawan Arewa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Na yi iyakan kokari na kuma ku shaida ne, Buhari Ga Al'ummar Yobe

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga al'ummar jihar Yobe su zabi duk shugaban da suke so kuma su rike amanar da Allah ya daurawa kowanne daga cikinsu.

Buhari ya bayyana hakan ne yayinda ya halarci taron yakin neman zaben jam'iyyar All Progressives Congress APC da ya gudana ranar Talata, 10 ga Junairu, 2023 a Damaturu.

Shugaban kasan ya bada tarihin yadda aka yi masa wulakanci iri-iri lokacin da yake neman shugabancin kasar Najeriya.

Ya ce shi ko kadan abin duniya bai damesa ba kuma nan da dan 'kankanin lokaci zai sauka daga mulki ya koma gida.

Yace:

"Ni na tashi maraya, ban san mahaifi na ba. Kuyi iyakan kokarinku ku biya amanar da aka baku da ta iyalin ku."

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Asirin Manyan Yan Takara Biyu, Yace Hatsari Ne Babba a Zabe Su a 2023

"Abin duniya abin banza, ku rike amana, ku rike jama'ar da ke karkashin ku."
"Na shekara 80, na yi aikin soja, na yi na ofis, na shiga siyasa, na nemi shugaban kasa sau uku, na shiga shari'a na ce a tausaya min, sai aka min dariya"
"Mu mun gama namu Insha'aLLahu, nan da wata biyar zamu koma gida."

Asali: Legit.ng

Online view pixel