Daga Karshe Dai Dokar Takaita Cire Kudi a Najeriya Ta Fara Aiki a Yau Litinin

Daga Karshe Dai Dokar Takaita Cire Kudi a Najeriya Ta Fara Aiki a Yau Litinin

  • Babban bankin Najeriya ya sanya sabbin dokoki da ke alaka da cire kudi a fadin kasar nan saboda wasu dalilai
  • A yau ne dokar takaita cire kudi ta fara aiki a Najeriya, kana an umarci bankuna su fara ba da sabbin Naira a injunan ATM
  • CBN ya sauya fasalin Naira, ya bayyana dalili tare da kawo sabbin dokokin da za su tafiyar da sabbin kudin da aka kirkira

Najeriya - A yau ranar Litinin 9 ga watan Janairun 2023 ne sabuwar dokar takaita cire kudi ta fara aiki a Najeriya tun bayan da aka bayyana sanya ta a shekarar da ta gabata.

Babban Bankin Najeriya (CBN) bayyana a baya cewa, ya kirkiri hanyar rage yawaitar yawon kudade a hannun jama’a domin tabbatar da ana amfani da hanyoyin biya daban-daban.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Fadawa Kamfanin NNPC Ya Rage Farashin Fetur a Najeriya

A dokar da CBN ya sanya, ya ce daidaikun mutane za su iya cire N500,000 ne a mako a bankuna ko injunan ciren kasar, BBC Hausa ta ruwaito.

Dokar kayyade cire kudi ta fara aiki a Najeriya
Daga Karshe Dai Dokar Takaita Cire Kudi a Najeriya Ta Fara Aiki a Yau Litinin
Asali: Getty Images

Hakazalika, an ba kamfanoni damar cire kudaden da suka kai N5,000,000 a cikin mako duk dai don areg yawon kudi a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya za a yi idan mutum ko kamfani na son cire fiye da adadin da aka kayyade?

Babban bankin ya ba da mafita ga duk wanda ke son cire kudi fiye da adadin da aka shar’anta a sama.

Ga daidaikun mutanen da ke son cire sama da N500,000, banki zai caji akalla 5% na adadin da za a cire.

Hakazalika, ga kamfanoni, duk mai son cire sama da N5,000,000, to tabbas zai ba da 10% na adadin da yake son cirewa ga banki.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu, Obi: CAN Ta Magantu Kan Yan Takarar Shugaban Kasa, Ta Fada ma Matasa Wa Za Su Zaba

A tun farko kun ji yadda CBN ya umarci bankuna da su daina ba da tsofaffin kudade a injunan cire kudi a fadin kasar nan.

Hakazalika, ya umarci kowanne banki da ya gaggauta fara sanya sabbin Naira a injunan cire kudi na kasar.

Wasu bankuna basu fara ba da sabbin kudi a ATM a ranar Litinin

Da yammacin ranar Litinin, wakilin Legit.ng Hausa ya ziyarci wasu injunan cire kudi a Commercial Area da ke jihar Gombe, inda ya zanta da wasu da ke bin layin cire kudi.

Idris Yahaya, wani da ya zo cire kudi a wani bankin da ke yankin ya shaida cewa:

"To gashi dai kana gani, na gabana tsoffin kudi ya cire 'yan N500, nima watakila su zan cire. A cikin banki ma ba cika ba da sabbin kudin ba gashi mutane na so balle kuma a ATM."

Ahmad Muhammad Sani, ya ce alamu sun nuna akwai karancin kudin a bankunan, don haka ba lallai ake samun wadatattun kudin ba mutane a ATM ba.

Kara karanta wannan

Akwai Isassun Sabbin Kudi A Bankuna, Bamu Hana Badasu a Kanta Ba: CBN Tayi Martani

Ya ce:

"Mutane sun matsu ne kawai, ya kamata 'transfer' ya bi jikinmu. Ana ta damuwa kan kudi, ai ba ana son su yi yawa bane, ana son ragewa ne, don haka babu bukatar dole sai an samu wadatattu a ATM da cikin bankin ma."

Kamfanin da ya buga sabbin Naira ya fadi dalilin sauya launi a madadi sake zubin halittar Naira

A wani labarin kuma, kamfanin da ya buga sabbin Naira ya ce, ya zabi sauya launin kudin ne a madadin yin sabon zubi don kare kudin.

Ya bayyana cewa, akwai sarkafe-sarkafe na tsaro da ke jikin sabon kudi, don haka ba abin kushewa bane.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kushe zubin kudin da kuma zargin ingancinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.