Matashi Ya Wallafa Hotunan Gidansa Da Aka Kera da Kwano, Akwai CCTV da Kayan More Rayuwa a Ciki

Matashi Ya Wallafa Hotunan Gidansa Da Aka Kera da Kwano, Akwai CCTV da Kayan More Rayuwa a Ciki

  • Wani matashi wanda yace shi kadai yake rayuwarsa ya wallafa hotunan gida mai daki daya da ya ginawa kansa
  • Yanayin yadda mutumin ya kawata cikin dakin ya burge mutane da dama inda suka ji sha’awar yadda ya rataye talbijin da shirya gadonsa
  • Daga cikin masu amfani da soshiyal midiya da suka yi martani, sun nemi sanin ko da gaske CCTV kamara ne a gidan nasa

Wani matashi mai suna Samuel ya sha jinjina a wajen mutane da dama kan yadda gidansa ya hadu lokacin da ya wallafa hotunan dakinsa da aka kera da kwanun zinki.

Yayin da mutum ke iya ganin yadda aka kewaye gidan da kwanon zinki, cikin gidan ya fi wajen kyau sosai. Mutane da dama sun kayatu matuka.

Matashi da gidan kwano
Matashi Ya Wallafa Hotunan Gidansa Da Aka Kera da Kwano, Akwai CCTV da Kayan More Rayuwa a Ciki Hoto: Samuel Mo-shoe
Asali: Facebook

Ya raba dakinsa biyu inda ya zama ciki da palo yayin da ya rataye talbijin dinsa a bango. Baya ga talbijin dinsa akwai firinji da abun dumama abinci. An mayar da wani bangare na dakin ya zama kicin dinsa.

Kara karanta wannan

Boka Ya Yi Mummunan Karshe, Ya Mutu a Wajen Lalata da Uwargidar Wani Fasto

A mashigin gidan akwai CCTV. Akwai kuma wata kamara a dakin saboda tsaro. Mutumin ya ce shi kadai yake zama.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Martanin jama’a

Tsundzukani Prosperity Baloyi ya ce:

“Ya yi kyau matuka.”

Nomazulu Cita ya ce:

“Wow! Ya burge! Zan iya kawo ziyara don kawai na zo na huta a wannan hadadden wuri mai tsafta.”

Gift Manzini ya ce:

“Abun ya burge matuka! Na so yadda cikin yake sannu da kokari.”

Sibongile Phakathi ya ce:

“Wow! Ya burge! Kamata yayi ka rungume kanka...wannan ya yi kyau, haduwa na daban...sannu sarkin tsafta.”

A wani labari na daban, wani uba ya fashe da kuka bayan diyarsa da ya kama tana aikata laifi ta yi masa alkawarin mota.

Magidancin dai ya gano diyar tasa labe a cikin kwaba tana tsotsa garin milo da ta tasa gwangwaninsa a gaba.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Wani matashi ya yi tsaurin ido, ya sace mahaifinsa, an ba kudin fansa N2.5m

Da ganin uban nata sai ta sha jinin jikinta inda ta ce kayanta take nema. Sai dai kuma ta bayar da hakuri ganin cewa an samuta da aikata laifin dumu-dumu.

Domin toshe masa baki, an jiyo yarknyar tana fada masa cewa za ta siya masa mota bayan ta ba da hakuri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel