Yobe: An Gibge Jami'an Tsaro Yayin da Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Damaturu

Yobe: An Gibge Jami'an Tsaro Yayin da Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Damaturu

  • Rahotani sun tabbatar da cewa an kara jibge jami'an tsaro a Damaturu gabanin isowar shugaban kasa Buhari ranar Litinin
  • Shugaban zai kai ziyara jihar Yobe gobe Litinin, 9 ga watan Janairu, 2023 domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka
  • Ana tsammanin Buhari zai bude sabbin ayyukan da suka shafi rundunar yan sanda da kuma na gwamnatin Mala Buni

Yobe - An kara tsaurara tsaro a Damaturu, babban birnin jihar Yobe yayin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai kai ziyara jihar ranar Litinin.

Wakilin hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a ranar Lahadi ya tattara cewa Dakarun rundunar 'yan sanda sun yi wa birnin tsinke tare da sauran jami'an hukumomin tsaro.

Shugaba Buhari.
Yobe: An Gibge Jami'an Tsaro Yayin da Shugaba Buhari Zai Kai Ziyara Damaturu Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa tulin jami'an tsaron sun mamaye muhimman wurarae a babban birnin jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Fitaccen Dan Takarar Shugaban Kasa Yace Zai Ji Tsoron Allah Idan aka Zabe Shi a 2023

Kakakin rundunar yan sandan Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ya shaida wa NAN cewa jami'an sun shirya tsaf da cikakkun kayan aiki domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro gabanin, lokacin da kuma bayan ziyarar Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane ayyuka shugaban kasa zai yi a Damaturu?

Yace mai girma shugaban kasa zai kaddamar da sabuwar hedkwatar 'yan sanda da aka gina, Asibiti da makarantar Sakandiren 'yan sanda a Damaturu.

Haka zalika ana tsammanin Buhari zai kaddamar da filin jirage masu dauko kaya, sabuwar makarantar zamani a rukunin gidajen New Bra Bra, sabon Asibitin yara da haihuwa da kuma kasuwar Damaturu.

Tun da farko, kwamishinan kasuwanci, masana'antu da wuraren bude Ido na Yobe, Alhaji Barma Shettim, yace kasuwar da Buhari zai bude ta kunshi manyan abubuwa na zamani.

Yace an kammala aikin zamanantar da kasuwannin Nguru da Gashuwa yayin da garin Potiskum aikin ya cimma kashi 65 cikin dari.

Kara karanta wannan

An Tsaurara Tsaro A Yola Babban Birnin Jihar Adamawa Gabanin Zuwan Shugaba Buhari Yakin Neman Zabe

An ce tuni fastocin Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa a APC, da na gwamna Buni suka mamaye gidan gwamnati da kuma Filin wasan August 27.

Shugabannin APC a Akwa Ibom suna munafuntar Tinubu

A wani labarin kuma Ministan Buhari da ya yi murabus ya ce akwai wasu jagororin APC dake cin amanar Tinubu a boye

Tsohon ministan Buhari kuma mataimakin shugaban kwamitin kamfen APC na kasa, Godswill Akpabio, yace wasu jiga-jigai suna yi wa Atiku aiki a boye.

Sanatan ya ce ya san wasu shugabannin APC a jihar ta Akwa Ibom, wadanda ke fadin Sai Asiwaju da rana amma da daddare su koma Atiku da PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262