Alkawari ya Cika: Sarkin Kano yayi Wuff da Tsohuwar Budurwarsa, An Daura Aure
- Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya aura tsohuwar zumarsa, Hauwa Adamu Abdullahi Dikko wacce aka fi sani da Hajiyayye
- An daura auren tsofaffin masoyan junan ne a ranar Juma’a, 6 ga watan Janairun 2023 wanda aka yi sama da shekara da fara batun auren
- Majiyar cikin gida ta tabbatar da daurin auren inda tace an yi shi ne babu wani babban shagali duba da cewa basaraken ba ya bukatar hakan
Kano - Allah ya yarda, alkawari ya cika tsakanin Hauwa Adamu Abdullahi Dikko wacce aka fi sani da Hajiyayye da Sarkin Kano, Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero.
Kamar yadda Legit.ng Hausa ta tattaro, an daura auren masoyan junan a ranar Juma’a da ta gabata, 6 ga watan Janairun 2022 a garin Kano.
Kamar yadda shafin @diaryyofnorthernwomen suka wallafa a Instagram, an daura auren basaraken mai daraja ta daya da Hauwa Adamu Abdullahi Dikko.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tun a shekarar 2021 dai Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa an fara shirin auren basaraken da Hajiyayye wacce tsohuwar budurwarsa ce tun kafin ya zama Sarkin Kano.
An rahoto cewa, tuni masarautar Kano da dangin amaryar da ke Dorayi suke shirin kulla auren sunnar.
Majiyoyi makusanta da gidan sarautar sun tabbatar da cewa babu wani shagalin da za a yi a bikin don basaraken ba ya so, yana don aure mara hayaniya.
An tattaro cewa, an daura auren a gidan marigayi Jarman Kano, Farfesa Isah Hashim, wanda ke Nasarawa GRA a jihar.
Alhaji Yusuf Nabahani Ibrahim, Madakin Kano, shi ne ya wakilci angon yayin daurin auren yayin da Alhaji Shehu Hashim ya zama waliyyin Amarya.
Sauran wadanda suka shaida daurin auren akwai Makaman Bichi, Alhaji Isyaku Umar Tofa da Sarkin Dawaki Mai Tuta.
Amaryar an gano cewa tsatson Malam Jamo ce, wanda ‘dan uwa ne ga marigayi Sarkin Kano, Ibrahim Dabo.
Legit.ng Hausa ta zanta da wata majiyar cikin gidan sarautar wacce bai dace a ji daga bankinta ba shiyasa ta bukaci a sakaya sunanta.
Ta Tabbatar da cewa an daura auren basaraken mai mata daya da ‘ya’ya hudu da galleliyar budurwar.
”Tabbas an daura auren Mai Martana da Hauwa wacce aka fi sani da Hajiyayye a ranar Juma’a da ta gabata.
”Wannan za mu iya cewa alkawari ne ya cika saboda Mai Martaba da Hajiyayye sun dade suna soyayya.
”Tun kafin hawansa gadon sarautar Dabo suke tare kuma sai yanzu Allah ya yarda. Tun kusan da shekara daya kenan da ake zancen auren. Da yake ba wani shagali za a yi ba, shiyasa kawai aka daura auren.”
- Majiyar ta tabbatar.
Sarkin Daura ya sake yin wuff da yarinya shakaf
A wani labari na daban, Sarkin Daura, Alhaji Dr Umar Faruk, ya aura yarinya danya shakaf mai shekaru 22 a duniya.
An gano cewa, an yi auren ne a watan Yulin 2022 ba tare da wasu manyan shagulgula ba.
Asali: Legit.ng