Ayiriri: Sarkin Daura ya sake yin wuff da budurwa mai shekaru 22, hotuna sun bayyana

Ayiriri: Sarkin Daura ya sake yin wuff da budurwa mai shekaru 22, hotuna sun bayyana

  • Sarkin Daura, Alhaji Dr Umar Faruk mai shekaru 91 ya kara yin wuff da budurwa danya shakaf mai shekaru 22
  • Kamar yadda aka tattaro, an daura auren ne ba tare da wasu manyan shagulgula ba a makon da ya gabata
  • Tuni dai amarya Aisha Gona Safana ta tare a dakinta inda ta tabbata sabuwar gimbiya kuma amaryar tsohon basaraken

Labari mai zafi da Legit.ng Hausa ke tattaro muku shi ne na yadda Sarkin Daura, Alhaji Dr. Umar Faruk ya sake yin wuff da budurwa danya shakaf mai shekaru 22 a duniya.

Kamar yadda @fashionseriesng suka bayyana, an yi bikin ne ba tare da wata hayaniya ba a makon da ya gabata.

Sarkin Daura
Ayiriri: Sarkin Daura ya sake yin wuff da budurwa mai shekaru 22, hotuna sun bayyana. Horo daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

Kara karanta wannan

Borno: Yan Boko Haram Sun Kai Wa Tawagar Shugaban Ƙaramar Hukumar Hari, Sun Kashe Ɗan Sanda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zukekiyar amaryar mai suna Aisha Gona Safana ta tabbata sabuwar gimbiya a Daura.

A shekara 90, Sarkin Daura ya auri tsaleliyar Amarya 'yar shekara 20

A wani labari na daban, Daily Nigerian na ruwaito cewa Mai Martaba Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, ya yi sabuwar Amarya, Aisha Iro Maikano, a ranar Asabar.

An tattaro cewa an yi daurin auren bayan dan gajeren lokaci da Sarkin ya hadu da yarinyar wacce diya ce ga Fagacin Katsina, Iro Maikano.

Hakazalika rahoton ya nuna cewa an daura auren bisa kudin sadaki N1million.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel