‘Yan Ta’adda Sun Kuma Kai Mugun Hari, Sun Dauke Mutane da-dama a Tashar Jirgin Kasa

‘Yan Ta’adda Sun Kuma Kai Mugun Hari, Sun Dauke Mutane da-dama a Tashar Jirgin Kasa

  • An tabbatar da ‘Yan ta’adda sun tsere da matafiya a tashar jirgin kasa da ke Igueben a jihar Edo
  • Mutane na zaune ana jiran jirgin kasan Warri, sai ‘yan bindiga suka duro, suka fara harbe-harbe
  • ‘Yan sanda sun ce fasinjoji da yawa sun samu rauni, ana kokarin ceto wadanda aka yi garkuwa da su

Edo - ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji da yawa daga tashar jirgin kasa da ke karamar hukumar Igueben a jihar Edo a karshen makon nan.

Rahoton Daily Trust ya nuna wadannan Bayin Allah da aka dauke su na shirin shiga jirgin kasan da zai je birnin Warri ne a lokacin da aka kawo harin.

Majiyoyi da-dama sun tabbatar da aukuwar wannan labari mara dadi a yammacin Asabar.

Jaridar ta ce babu tabbacin ko wasu sun rasu sa a sanadiyyar harin, amma shakka babu akwai wadanda suka samu rauni a dalilin harbin bindigogi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Mazauna sun rikice, an sace musu mai gidan saukar baki

Jami’in hulda da jama’a wanda yake magana da yawun bakin rundunar ‘yan sandan reshen jihar Edo, Chidi Nwabuzor ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Nwabuzor ya ce wadannan miyagu sun aukowa tashar jirgin ne dauke da bindigogin AK-47 a ranar Asabar da yamma, sai suka rika harbe-harbe ko ta ina.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tashar Jirgin Kasa
Jirgin kasa a Najeriya Hoto: thenewsguru.com
Asali: UGC

Bayan sun razana jama’a, jami’in ‘dan sandan ya ce ‘yan bindigan suka yi awon-gaba da matafiya.

Jawabin jami’an tsaron ya nuna cewa an baza dakaru domin gaggawar ceto wadanda aka dauke daga hannun wadannan masu garkuwa da mutane.

Punch ta ce harin yana zuwa ne watanni bayan an tare jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a wani kauye mai suna Katari, inda aka yi garkuwa da fasinjoji.

Rahoton da aka fitar cikin daren Lahadin nan ya tabbatar da cewa harin ya raunata mutane da yawa. Sai dai babu adadin wadanda ta’adin ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Dan Siyasa Da Wasu Mutane Uku a Wata Jahar Kudu

Jawabin jami'an 'yan sanda

“Ana masu sanar da manema labarai cewa yau, 7 ga Junairun 2023 da kimanin karfe 4:00 na yamma, ‘yan bindiga dauke da AK-47 suka kai hari a tashar jirgin Igueben a jihar Edo.
Sun yi garkuwa da fasinjojin da ba a san adadinsu ba da ke kokarin shiga jirgi zuwa Warri.
‘Yan bindigan sun rika harbin iska kafin su dauke wasu fasinjoji, kuma su bar wasu mutanen da rauni. Shugaban ‘yan sand ana Irrua, DPO na Igueben da jami’ansu sun ziyarci wurin tare da dakarun Edo SSN, ‘yan banga da nufin a kare rayuwa da dukiyar sauran fasinjojin.
An soma tsefe jejin da nufin a ceto mutanen da aka yi awon gaba da su, sannan a damke masu garkuwa da mutanen. Za a sanar da ku game da duk wani cigaban da aka samu nan gaba.

- SP Chidi Nwabuzor

Inganta tsaro a jiragen kasa

Kwanakin baya an samu labari Ministan sufuri na kasa, Mu’azu Sambo yace duk wanda bai da lambar waya da NIN ba zai hau jirgin Kaduna-Abuja ba.

Injiniya Mu’azu Sambo yace daga yanzu babu karamin yaron da za a saidawa tikitin jirgin kasa, sai dai matashi ya tsaya masa domin a tabbatar da tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng