Gobara Ta Tashi A Wani Katafaren Rukunin Shaguna A Kasuwar Anambra, An Tafka Asarar Dukiya

Gobara Ta Tashi A Wani Katafaren Rukunin Shaguna A Kasuwar Anambra, An Tafka Asarar Dukiya

  • Yan kasuwa sun tafka mummunan asara sakamakon gobara da ta faru a babban kasuwar Relief da ke birnin Onitsha a jihar Anambra a kudu maso gabas
  • Wasu wanda abin ya faru a idonsu sun ce wutar ta tashi ne a wani shago a rukunin shagunan daga nan kuma ta bazu zuwa sauran shaguna
  • An tuntubi shugaban hukumar kashe gobara na jihar, Mr Martin Agbali, don ji ta bakinsa amma bai amsa ba sai dai an ga jami'an kashe gobara suna aiki

Jihar Anambra - Gobara ta tashi a wani babban kanti da ke kusa da kasuwar Relief da ke birnin Onitsha na jihar Anambra, rahoton The Punch.

Kawo yanzu ba a san abin da ya yi sanadin tashin gobarar ba, amma akwai kayayyakin biliyoyin naira a kantin mallakar yan kasuwa da ba su riga sun dawo daga hutun kirsimeti da sabuwar shekara ba.

Kara karanta wannan

Daga Shigowa Shekarar 2023, Kamfonin Lantarki Sun Yi Karin Farashin Wuta a Boye

Kasuwar Onitsha
Gobara Ta Tashi A Wani Katafaren Rukunin Shaguna A Kasuwar Anambra, An Tafka Asarar Dukiya. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a samu cikakken bayani kan afkuwar gobarar ba a yanzu, amma wasu shaidun gani da ido sun ce gobarar ta tashi ne daga wani shago a rukunin shagunan.

Shugaban hukumar kashe gobara na jihar Anambra, Mr Martin Agbali, bai amsa wayarsa ba da aka kira shi, kuma bai amsa sakon kar ta kwana ba.

Amma, an ga jami'an hukumar kashe gobarar tuni sun isa wurin da abin ya faru suna kokarin kashe wutan a lokacin hada wannan rahoton.

Wannan shine karo na biyu da ake samun gobara a kasuwa a jihar ta Anambra cikin yan watanni.

Gobara ta lukume shaguna guda 252 a kasuwar Galadima da ke Abuja

A wani labarin daban, Daily Trust ta rahoto cewa a kalla shaguna guda 252 ne suka kone sakamakon mummunan gobara da ta faru a kasuwar Galadima da ke Gwarimpa a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Daga Jin Dumi Ashe Karshensu Ne Yazo, Yadda Wasu yan gida suka rasa ransu

Wata mata cikin wadanda shagunanta suka kone a gobarar, Fatima Abubakar, wacce ke da gidan cin abinci da kanti a kasuwar ta ce ta rasa komai.

A cewarta, lamarin ya faru misalin karfe 1.30 na rana, a lokacin da musulmi ke tafiya wurin ibada, su kuma mabiya addinin kirista suna hutun kirsimeti.

Shima wani tela da abin ya shafa ya ce keken dinkinsa da wasu kayan mutane duk sun kone kurmus a gobarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164