Najeriya Za Ta Shaida Hazo Mai Yawa Na Tsawon Kwanaki 3 Daga Ranar Juma’a, NiMet

Najeriya Za Ta Shaida Hazo Mai Yawa Na Tsawon Kwanaki 3 Daga Ranar Juma’a, NiMet

  • Hukumar NiMet ta bayyana yanayin da Najeriya za ta shiga cikin kwanaki uku masu zuwa
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da hunturu ke kara shigowa da kuma yadda hazo ke kara yawa
  • Hukumar ta ba ‘yan Najeriya shawari kan hanyoyin da za su bi don ganin sun shawo kan wannan lamarin

FCT, Abuja - Hukumar hasashen yanayi a Najeriya (NiMet) ya hango aukuwar hazo mai tsanani daga ranar Juma’a 6 ga wata zuwa Lahadi 8 ga watan Janairu a fadin kasar.

Wannan na kunshe ne a cikin takardar kasashen yanayi da NiMet ya fitar a makon a babban birnin tarayya Abuja, PM News ta ruwaito.

A cewar rahoton NiMet, jihohi daga Arewacin Najeriya da suka hada da Yobe, Kano, Katsina da Jigawa za su ga faruwar hazo mai kaurin 1,000m a kwanakin.

Kara karanta wannan

An Kama Amina Guguwa Yar Shekara 50 Kan Kashe Kishiyarta Yayin Dambe A Bauchi

NiMet ta bayyana hazon da 'yan Najeriya za su gani a makon nan
Najeriya Za Ta Shaida Hazo Mai Yawa Na Tsawon Kwanaki 3 Daga Ranar Juma’a, NiMet | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Hakazalika, sauran jihohin yankin na Arewa, manyan birane da yankunan Kudanci za su ga hazon da ya kama daga kaurin 1,000m zuwa 5,000m.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jihohin Kwara da Oyo kuwa, za su shaida kazon da ya yi kasa da 1,000m, kamar yadda hasashen ya nuna cikin kwanakin uku masu zuwa.

Kowa ya dauki matakin da ya dace

Saboda haka ne hukumar take shawartar ‘yan Najeriya da su dauki matakan kariya don iya magance matsalolin da ke tattare da wannan yanayi, Punch ta ruwaito.

Ga masu matsalar numfashi, an bukace su da yin amfani da kayayyakin da za su hana su mu’amalantar kura da hazo saboda yanayin da suke ciki na rashin lafiya.

Ga batun yanayin sanyi da za a gani a kwanakin, NiMet ta ce, yaba da kyau kowa ya yi shirin amfani rigunan sanyi, safa da bargo.

Kara karanta wannan

2023: Magana Ta Kare, Wike da Ortom Sun Hada Baki, Sun Yi Magana Kan Dan Takarar da G5 Zata Marawa Baya

A bangare guda, an shawarci kamfanonin jiragen sama da su dakata da zirga-zirga da keta hazo cikin kwanakin har sai yanayin ya koma daidai.

A daina kwana da garwashi a daki, inji masana lafiya

A wani labarin kuma, masana lafiya sun ba ‘yan Najeriya shawari kan abin da ya kamata su yi a lokacin da ake sanyi da hunturu.

Hakazalika, sun gargadi jama’a kan kwana da garwashin wuta a cikin daki yayin da ake tsaka da sanyi.

A bangare guda, an tattaro gawarwakin wasu ma’aurata da ake zargin sun mutu ne bayan da suka yi amfani da garwashin wuta a daki ya kwana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.