Daga Shigowa Shekarar 2023, Kamfonin Lantarki Sun Yi Karin Farashin Wuta a Boye

Daga Shigowa Shekarar 2023, Kamfonin Lantarki Sun Yi Karin Farashin Wuta a Boye

  • Kamfanonin da ke da alhakin raba wuta a gidajen mutane sun kara farashin sayen lantarki a Najeriya
  • An yi wannan kari ne a mafi yawan wureare ba tare da kamfanonin sun yi wa jama’a wani bayani ba
  • Da jama’a suka farga da tashin faashin, kamfanin AEDC ya ce hukumar NERC ta ce ayi karin farashin

Abuja - Kamfanonin da ke raba wutar lantarki a Najeriya, sun yi wani karin farashi a boye a fadin kasar nan, ba tare da sun sanar da jama’a ba.

Punch ta bankado karin da aka yi, ta ce mafi yawancin kamfanonin DisCos na kasar nan, ba su bada sanarwar canjin farashin da aka samu ba.

Sai dai mutane da ke shan wutan lantarkin a gidaje da wuraren aiki, sun koka a kan wannan kari da aka yi a lokacin da ake cikin matsin lamba.

Kara karanta wannan

Tsantsar fikira: Bidiyon yadda matashi ya kera motar da ba a taba ganin irinta ba, ya tuka ta

Jama’a su na ganin ana cigaba da lafta masu tsadar wutan ne a lokacin da samun lantarkin yake wahala, bugu da kari kaya su na dada tsada.

Abin N66 ya dawo N72

Wasu mazauna garin Legas da aka zanta da su, sun bayyana cewa yanzu an koma saida kowane balli na wutar lantarki a kan N72.2, daga N66.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce kamfanin Ikeja Disco ya sake yin karin farashi bayan karin da aka yi a baya.

Lantarki
Na'urorin bada lantarki Hoto: www.esi-africa.com
Asali: UGC

Jama’a su na cewa ba a sanar da su kudin shan wutan ya tashi ba, sai dai kurum suka ga farashin da suka saba sayen lantarkin ya yi sama.

Wani Oyibo Ediri da yake amfani da kamfanin AEDC ya yi magana a Twitter, ya ce an kara masu farashin sayen lantarki daga N57.55 zuwa N68.2.

Umarnin NERC ne - DisCos

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Bindiga Sun Kutsa Dakin Otel Sun Sace DPO A Wata Shaharariyar Jihar Arewa

Da kamfanin raba wutan suka tashi ba shi amsa, sai suka ce an daga farashin ne bayan umarni da suka samu daga hukumar NERC ta Najeriya.

Amma rahoton News Telegraph ya nuna babu wata sanarwa da ta fito daga NERC mai kula da harkar wuta a kasar a kan wani sabon karin farashi.

A farkon shekarar da ta gabata, hukumar ta sanar da al’umma kamfanoni 10 da ke raba wuta za suyi karin akalla 5% zuwa 12% a kudin saida wuta.

Jaridar ta nemi jin ta bakin masu magana da yawun kamfanonin Eko Electricity, Ikeja Electric, da Ibadan DisCos, amma ba su iya cewa komai ba.

Neman fetur a Arewa

Nan da wasu shekaru nan gaba, kun ji labari cewa babu mamaki a daina yi wa Arewa gorin man fetur domin akwai yiwuwar hako rijiyoyi a yankin.

Bayan Gombe da Bauchi, ma’aikatan NNPC su na bidar mai a shiyyar Bida, Keana, Wadi a jihohin Arewacin kasar nan irinsu Neja, Yobe, da Nasarawa.

Kara karanta wannan

Yadda Wani Matshi Da Yaje Ba Haya A Dawa Karke Da Fada Da Damisa Wadda Ta Jikkatashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng