Bacci Suke a Ko’ina: Karamar Yarinya Ta Bingire Da Bacci a Tsaye, Bidiyon Ya Yadu

Bacci Suke a Ko’ina: Karamar Yarinya Ta Bingire Da Bacci a Tsaye, Bidiyon Ya Yadu

  • Yayin da take tsaye a wajen daki, an gano wata yarinya ta bingire da bacci har ta kusa faduwa kasa ba don ta kama jikinta ba
  • A wani bidiyo da aka wallafa a manhajar TikTok, an gano yarinyar tana sharar bacci kamar ta samu katifa mai laushi
  • Bidiyon da aka wallafa a watan Disambar 2022 ya ba mutane da dama mamaki domin tuni ya yadu kuma an samu fiye da mutum 132k da suka kalla

Masu amfani da TikTok sun yi martani a kan bidiyon wata yarinya da ta bingire da bacci mai nauyi yayin da take tsaye a kofar gida.

Yarinyar ta manta da kanta gaba daya sannan ta kama bacci kamar wacce ke kwance a kan katifa.

Karamar yarinya na bacci a tsaye
Bacci Suke a Ko’ina: Karamar Yarinya Ta Bingire Da Bacci a Tsaye, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@lifewiththetwins7.
Asali: UGC

Yanayin yadda ta tsaya a bidiyon mai tsawon sakan 8 da shafin @Momof4kids ya wallafa ya haifar da martani masu ban dariya a tsakanin masu amfani da TikTok.

Kara karanta wannan

Bidiyon Matar Aure Tana Gaggawar Ba Miji Abinci a Baki Kada ya Makara Aiki ya Janyo Cece-kuce

Bidiyon karamar yarinya tana bacci a tsaye

Ba a jima ba sai kafar yarinyar ya fara rawa alamun dai magagin bacci kuma har ta kusa faduwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma mutane da dama sun ji mamakin yadda har ta iya rike kanta yayin da take tsaye ba tare da ta fadi ba.

Bayan ta kama jikinta tare da juyawa daya bangaren, sai ta ci gaba da baccinta.

Mutane da dama da suka ci karo da bidiyon sun ce wannan ba sabon abu bane a wajen yara yin bacci a yanayi mai ban mamaki.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Zion ya ce:

"Yi bacci da daddare kin ce ba haka ba. Kin zata ni kike yiwa? Kan ki kike yiwa."

@rock2sha ta yi martani:

"Ta yi kama da tagwayen sosai."

@Tekas_chops ta ce:

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Bidiyon Yadda Wani Yaro Ya Dafi Babbar Waya Ya Koma Kamar Babban Oga Ya Ja Hankali

"Allah ya baki yan wasan barkwanci masu kyau. Babu lokacin kadaici a wannan gidan."

@marthawinnie6 ta yi martani:

"Ni kenan a duk lokacin da littafi ya bayyana a gaba na."

@hajiafati513 ta ce:

"Kin zata kina da wayo ne."

Hotunan kyakkyawar yarinya da idanu masu launin shudi

A wani labarin kuma, jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da hotunan wata kyakkyawar yarinya yar baiwa.

Yarinyar mai suna Wasilat mai shekaru 7 a duniya tana dauke da wasu irin idanu masu sheki da launin shudi kuma da su aka haifeta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel