Bidiyon Matar Aure Tana Ba Mijinta Abinci a Baki Tamkar Karamin Yaro, Ya Kayatar

Bidiyon Matar Aure Tana Ba Mijinta Abinci a Baki Tamkar Karamin Yaro, Ya Kayatar

  • Kamar yadda uwa ke tarairaiyar 'diyarta, an ga wata mata na ba mijinta abinci a baki yayin da ya shirya tsaf zai tafi wurin aiki da safe
  • An ruwaito yadda mutumin ya kusa lattin wurin aiki, amma duk da haka matarsa tana so yayi kalaci kafin ya tafi
  • Kaunar da matar ke nunawa mijinta da ya bayyana a bidiyon ya narkar da zuciyoyin jama'a yayin da yayi yawa a yanar gizo

Wani bidiyon wata mata cike da kauna taba ba mijinta abinci a baki saboda ya kusa lattin zuwa aiki ya jawo cece-kuce a yanar gizo.

Mata da Miji
Bidiyon Matar Aure Tana Ba Mijinta Abinci a Baki Tamkar Karamin Yaro, Ya Kayatar. Hoto daga LinkedIn/Sam'an Ali Mu'azu
Asali: UGC

Faifan bidiyon mai taba zuciya wanda Ali Mu'azu ya wallafa a LinkedIn gami da jinjinawa matar.

A cewar Ali, kowanne mutum ya cancanci mace ta gari a rayuwarsa, ko da kuwa matar abokiyarsa ce kawai.

Kara karanta wannan

"Nan Zan Kwana" Bidiyon Yadda Wani Mutumi Ya Gigita Diyarsa Yayin da Ya Shiga Dakin Tsohuwar Matarsa Ya Tube Kaya

Ya kara da cewa, mace ta gari tana kara kima ga rayuwar namiji ko a wanne matsayi ta tsaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A faifan bidiyon, matar daure da zani ta zauna gaban mijin yayin da shi kuna ya shirya tsaf.

Haka zalika, itama taba ci daga abincinsa. Baya ga bashi abincin da take, ta hada mishi da ruwan gora inda daga bisani ya bar wurin.

Martanin jama'a

Adam ya ce:

"Hakan yayi kyau. Naso a ce ni ne shi. Ina rokon addu'arku don in samu mace ta gari."

Okeowo Adeboye Opeyemi ya ce:

"Macen wannan shekarar."

Bright Richard ya ce:

"Wannan shi ne sakamakon abota a aure. Hakan yafi komai dadi. Bai damu da matsayi ko kudi ba."

Lanre Adeoye ta ce:

"Hakikanin gaskiya kenan, zan so dukkan maza su kula da matansu kamar sarauniyoyi yadda suma za a kula dasu kamar sarakuna. Sannan, idan Ubangiji ya baka mace ta gari ya kamata ya rike ta da karfi."

Kara karanta wannan

Miji Ya Manta Da Matarsa A Hanya Bayan Ta Sauka Kama Ruwa

Fatima Hussaini ta ce:

"Shi ne tushen farin cikin kowanne gida, duk mace na bukatar miji nagari ita ma."

Boniface Alimwebe ya ce:

"Amma cikin kwanakin nan aka dauko bidiyon? Ina ga irin wadannan matan babu su a al'ummanmu."

A kan bashi, asibiti sun rike jaririya a Delta

A wani labari na daban, wata mahaifiyar tagwaye ta koka kan yadda wani asibitin kudi ya rika mata diyarta saboda gaza biyan kudin magani.

Ta sanar da cewa, wani asibitin kudi ne suka tura su amma kuma sun sanar cewa basu da halin biyan makuden kudin da suka tunkari dubu dari hudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel