'Yar Wazirin Bauchi Ta Yi Murabus A Matsayin Kwamishina Bayan Gwamnan Bauchi Ya Tube Rawanin Mahaifinta

'Yar Wazirin Bauchi Ta Yi Murabus A Matsayin Kwamishina Bayan Gwamnan Bauchi Ya Tube Rawanin Mahaifinta

  • Kwamishinan Gama Kai da Kananana Masana'antu na jihar Bauchi, Hajiya Sa'adatu Bello Kirfi ta ajiye aikinta jim kadan bayan Gwamnan Bauchi ya tube rawanin mahaifinta
  • Hajiya Sa'adatu ta bayyana hakan ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata na 4 ga watan Janairun 2023 da ta aikwa wa sakataren gwamnatin jiha
  • Shima Babban mataimakin gwamna na musamman kan harkokin kananan hukumomi, Harsunu Yunusa Guyaba ya ajiye aikinsa

Jihar Bauchi - Hajiya Sa'adatu Bello Kirfi, kwamishinan Gama Kai da Kananana Masana'antu na jihar Bauchi ta yi murabus daga mukaminta.

Hakan na zuwa ne bayan da gwamnan jihar Bauchi ya kori mahaifinta, Alhaji Bello Kirfi daga sarautarsa na Wazirin Bauchi.

Radio Nigeria
'Yar Wazirin Bauchi Ta Yi Murabus A Matsayin Kwamishina Bayan Gwamnan Bauchi Ya Tube Rawanin Mahaifinta. Hoto: Radio Nigeria
Asali: Facebook

Wasikar da sakataren masarautar Bauchi ya rattaba wa hannu ta ce an tsige Kirfi ne daga mukaminsa kan 'rashin biyayya da girmama' gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.

Kara karanta wannan

Sarkin Bauchi ya Tsige Mutumin Atiku daga Sarautar Waziri a Dalilin Rikici da Gwamna

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wasikar nata mai dauke da kwanan wata na 4 ga watan Janairu, Sa'adatu ta yi godiya ga gwamna bisa bata damar aiki a gwamnatinsa, amma bata bayyana dalilin murabus din ba.

Wasikar ta Sa'adatu ta ce:

"Mai girma, ina son mika murabus dina a matsayin mamba na majalisar zartarwa na jihar Bauchi da kwamishina na ma'aikatar Gama Kai da Kananana Masana'antu na jihar Bauchi nan take.
"Ina son gode wa mai girma gwamna bisa damar da ya bani na yin aiki a karkashin gwamnatinsa."
Takardar Murabus
'Yar Wazirin Bauchi Ta Yi Murabus A Matsayin Kwamishina Bayan Gwamnan Bauchi Ya Tube Rawanin Mahaifinta
Asali: UGC

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin a Bauchi, kuma ta nemi a sakaya suna ta fada wa Legit.ng Hausa cewa murabus din nata ba zai rasa nasaba da tsige mahaifinta ba.

Majiyar ta kuma ce akwai yiwuwar wasu jiga-jigan gwamnati a Bauchin su ajiye aikinsu don nuna goyon baya ga Wazirin.

Kara karanta wannan

Sarkin Bauchi Ya Kori Wazirinsa, Na Hannun Daman Atiku, Bello Kirfi, Kan Rashin Biyayya Ga Gwamnan Bauchi

Majiyar ta yi ikirarin cewa akwai sarakuna da dama a jihar da basu goyon bayan tazarce na gwamnan kan zarginsa rashin gamsuwa da salon mulkinsa da suka ce yan uwansa da na matarsa kawai ya ke fifitawa.

A cewarta:

"Gaskiya mafi yawan al'ummar Bauchi ta sarakuna ba su tare da mai girma gwamna a yanzu. Shi ya bata rawansa da tsalle. Babu masu more romon demokradiyya a jihar sai iyalansa da dangin matansa.
"Akwai wasu murabus din da za su taho ma daf da zabe kawai lokaci ake jira."

Babban mataimakin gwamna na musamman kan harkokin kananan hukumomi na Bauchi ya yi murabus

Hakazalika, Harsunu Yunusa Guyaba, Babban mataimakin gwamna na musamman kan harkokin kananan hukumomi na Bauchi ya yi ajiye aiki.

Guyaba ya sanar da hakan ne cikin wata wasika da ya aika ga gwamnan Bauchi ta hannun sakataren gwamnati mai kwanan wata na 3 ga watan Janairu, ta Legit.ng Hausa ta gani.

Kara karanta wannan

"Ba Zan Hakura Ba" Gwamnan Arewa Da Aka Yi Wa Ruwan Duwatsu Ya Magantu

Takardar Murabus
'Yar Wazirin Bauchi Ta Yi Murabus A Matsayin Kwamishina Bayan Gwamnan Bauchi Ya Tube Rawanin Mahaifinta.
Asali: UGC

Guyaba shima bai bayyana dalilin murabus dinsa ba kuma ya yi godiya ga gwamna bisa damar da ya bashi.

Sarkin Bauchi ya tube wazirinsa Bello Kirfi kan rashin biyayya ga gwamna

Tunda farko, kun ji cewa masarautar Bauchi ta sauke Alhaji Bello Kurfi daga mukaminsa na waziri.

Hakan na zuwa ne bayan zargin rashin 'biyayya da girmama' gwamna da aka masa cikin wata wasika da ta fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164