Boka ya Yanke Jiki ya Fadi Yayin da Yake 'Shagalinsa' da Matar Fasto a Otal

Boka ya Yanke Jiki ya Fadi Yayin da Yake 'Shagalinsa' da Matar Fasto a Otal

  • Wani mutumi da aka gano boka ne ya yanke jiki tare da faduwa matacce dakin wani otal dake Ikere a jihar Ekiti yayin da yake sharholiya da wata mata
  • Lamarin ya faru a ranar Litinin da ta gabata kuma an gano cewar matar wani fasto ne da ke da coci a yankin
  • Tuni dai 'yan sanda suka cafke matar inda aka kwashi gawar bokan zuwa ma'adanar gawawwaki dake asibiti

Ekiti - Wani mutum mai matsakaicin shekaru ya yanke jiki ya fado tare da mutuwa bayan kammala sharholiyarsa da wata mata a otal dake Ikere Ekiti, hedkwatar karamar hukumar Ikere dake jihar Ekiti.

Majiyoyi sun ce lamarin ya faru ne a wani dakin otal inda mutumin wanda aka gano boka ne ya je ya samu matar a ranar Litinin, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Fitaccen Sarki a Arewa, Sun Tafka Ta'asa

Taswirar Ekiti
Boka ya Yanke Jiki ya Fadi Yayin da Yake 'Shagalinsa' da Matar Fasto a Otal. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Daya daga cikin majiyoyi, wacce mace ce da ta bukaci a boye sunanta, tace matar ta wani fasto ce a yankin wanda ya mallaki cocin kansa.

Tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mutumin ya mutu a dakin otal yayin da yake lalata da matar. Matar da kanta ta fasa ihu bayan ta gane cewa ya mutu.
"Manajan otal din da wasu mazauna yankin sun hanzarta zuwa wurin kuma da gaggawa aka dauka mutumin aka kai asibiti mafi kusa inda aka tabbatar da mutuwarsa."

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace rundunar ta fara bincike kan musabbabin mutuwar mutumin, jaridar Vanguard ta rahoto.

Abutu yace:

"Mun tabbatar da mutuwar wani mutumi a daya daga cikin otal din Ikere Ekiti a ranar Litinin. Gawarsa an dauke ta tare da adana ta a ma'adanar gawawwaki.

Kara karanta wannan

An Samu Babbar Matsala: Wasu Jiragen Sama Sun Yi Karo a Sararin Samaniya, Rayuka Sun Salwanta

"Muna tuhumar matar da lamarin ya ritsa da ita yayin da muke binciken abinda ke tattare da mutuwar mutumin."

Daga rabon fada, matashin Bakano ya rasa hannunsa

A wani labari na daban, jarabawa ta fadawa wani matashi mai suna Salisu Hussaini wanda ya rasa hannunsa kacokan daga zuwa rabon fada.

Fada ya kacame tsakanin mutum biyu wadanda suke zama a yankinsu kuma suke barazanar halaka junansu.

Namama ya nemi soka masa wuka a ciki amma ya kare da hannunsa wanda hakan yasa ciwo ya samu har aka cire hannun kacokan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel