Abun Alhini: Amarya da Ango Sun Gwabza Hatsarin Bayan Dawowa Daga Daurin Aurensu
- Wani mutumi 'dan Najeriya da matarsa sun rasa rayukansu bayan tafka mummunan hatsarin kan titi a hanyarsu ta dawowa daga daurin aurensu
- Ma'auratan, Mr da Mrs Akimu sun rasa rayukansu a ranar aurensu, wanda aka yi bikin gargajiyarsu cike da murna da farin ciki
- Hotunan mamatan ma'auratan kuma masoyan junan wani Haruna Barimoh ne ya wallafa a shafinsa na Twitter cike da kunar rai da jimami
Mutuwa ta datse labarin soyyayar wasu ma'aurata bayan sun rasu a ranar aurensu. An gano yadda ma'auratan suke kan hanyar dawowarsu daga shagalin bikinsu, yayin da suka tafka hatsari.
Hotunan mutumin da matarsa, Mr da Mrs Akimu yayi yawo a dandalin Twitter.
Haruna Braimoh ne ya wallafa labarin a shafinsa na Twitter wanda ya ce lamarin mara dadi ya faru ne a anguwar shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda Haruna ya rubuta:
"Wani labari mara dadi da ya faru a anguwar mu. Mariganya Mr da Mrs Akimu. Kun yi aure jiya kuma dukkanku kun koma ga Ubangiji a jiya kan hanyarku ta dawowa daga wajen bikin ku. Allah yasa aurenku dadi har a Aljannar Firdausi."
Jama'a sun yi martani
Masu amfani da kafar Twitter da dama sun bayyana damuwarsu da alhini game da labarin mara dadi, wanda suka siffanta da abun tausayi.
Martanin masu amfani da kafar sada zumuntar Twitter
@Mr_ibiang ya ce:
"Ubangiji ka ji kansu."
@iam_samorai yayi martani:
"Bawan Allah, wannan abu da ban tausayi!"
@amdalatShukuran ta ce:
"Ba zan ma iya kwatanta yadda danginsu za su kasance ba yanzu. Kidimewa za su yi a kalla. Ubangiji ya gafarta musu, kuma ya ba danginsu hakurin jure rashinsu."
@Freeman2gud yayi tsokaci:
"Labari mai tada hankali. Ubangiji ya yafe musu kura-kurensu, sannan ya sa su a Aljannar Firdausi."
@alphakenneth ya ce:
"Wannan da ban tausayi! Ubangiji Allah ya gafarta musu kura-kurensu."
@adunni_tmo tayi tsokaci:
"Subhanallah!!! Wannan labarin da ban tausayi!!! Allah ya amince musu shiga Aljanna tare da yafe musu kura-kurensu."
Taron aure ya watse kan Maggi da Maltina
A wani labari na daban, wani taron aure ya tarwatse bayan dangin angon sun ki kawo maggi da maltina a cikin kayan jerin sadakin.
Duk da jama'a da aka tara cincirindo, an watsa lamarin tare da fasa auren inda kowa ya kama gabansa.
Asali: Legit.ng