Kotu Ta Raba Ango da Amarya Watanni Kalilan Bayan Daura Masu Aure a Kaduna

Kotu Ta Raba Ango da Amarya Watanni Kalilan Bayan Daura Masu Aure a Kaduna

  • Kotun Shari'ar Musulunci a Kaduna ta rugaza auren watanni uku tsakanin Muhammad Abdulganiyu da Ma'arufat Ibrahim
  • Mai Shari'a Malam Rilwanu Kyaudai yace Kotu ta yi iya bakin kokarinta wurin ganin an samu masalaha amma abu ya ci tura
  • Ya umarci Amarya ta maida wa tsohon mijinta kuɗin sadaki da Akwatuna da wasu kayayyaki

Kaduna - Kotun shari'ar Musulunci mai zama a Magajin Gari, Kaduna ta raba aure tsakanin Muhammad Abdulganiyu da Ma'arufat Ibrahim.

Da yake bayyana hukuncin da Kotu ta yanke, mai shari'a Malam Rilwanu Kyaudai ya ce an rushe igiyoyin auren ne bayan duk yunkurin Kotu da magabata na sasanta ma'auratan ya ci tura.

Kotun shari'a
Kotu Ta Raba Ango da Amarya Watanni Kalilan Bayan Daura Masu Aure a Kaduna
Asali: Facebook

Alkalin ya umarci Ma'arufat Ibrahim ta maida wa tsohon mijinta sadakin da ya biya lokacin aurensu watau N20,000, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Imo: Tsohon Gwamna da Yaransa 2 Sun Kubuta daga Halaka, Ya Bayyana Yadda Lamarin ya Faru

Malam Rilwanu Kyaudai ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bayan haka zata dawo da Akwatun auren da ta karba da kayayyakin dake ciki amma banda wadan da ta riga ta fara amfani da su."
"Ba zata maido da wayar salula ba kamar yadda mai kara ya bukata amma zata dawo masa da Zoben Azurfan da ya siya mata."

Yadda ma'auratan suka yi cece-kuce a zaman Kotu

Tun da farko a cikin karar da ya shigar, Abdulganiyyu ya zargi amaryarsa da barin gidan aurenta ba tare da neman izininsa ba.

"Ina bakin kokarina wajem sauke hakkinta amma ita da mahaifiyarta ba su gani. Ba su yaba wa kokarin da nake yi kuma watanni uku kacal da daura mana aure."
"Idan bata sha'awar zaman aure da ni ta biya duk abinda na kashe a hidimar aurenta kuma ta dawo mun da wayar tarho da zoben azurfa da na siya mata."

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Fitaccen Sarki a Arewa, Sun Tafka Ta'asa

A bangarenta, Amarya Ma'arufat ta shaida wa Kotu cewa ta gudu ta bar gidan mijimta ne saboda ba ya iya ciyar da ita.

Ta kuma ƙara da cewa da bakinsa ya fada mata cewa ya aureta ne kawai saboda mahaifiyarsa ta umarci ya yi hakan.

A wani labarin kuma Kwana Hudu da Aure, Amarya Ta Kama Angonta da Yar Uwarta Suna Jin Dadi a Gado

Sabuwar amaryar da abun ya sosa wa zuciya, tace lamarin ya taɓa ta yadda ta koma Otal na tsawon mako ɗaya ba wanka da yawo.

Matar ta ƙara da cewa ta toshe lambar mahaifiyarta da kuma lambar Surukarta saboda sun roki ta yafe wa mutanen biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262