Harin 'Yan Bindiga: Yadda ni da 'Ya'yana Muka Sha da Kyar, Tsohon Gwamna

Harin 'Yan Bindiga: Yadda ni da 'Ya'yana Muka Sha da Kyar, Tsohon Gwamna

  • Ikedi Ohakim, tsohon gwamnan jihar Imo ya bada labarin yadda makasan haya suka yi yunkurin kai shi lahira tare da yaransa biyu
  • Ya sanar da yadda miyagun suka budewa motarsa wuta da harsasai kuma suka dinga harbin tayoyi bayan sun tsere amma Ubangiji ya tseratar dasu
  • Cike da takaici ya sanar da rashin daya daga cikin direbobinsa da wasu mutum uku wanda yace hakan ya matukar gigita shi

Imo - Tsohon Gwamna Ikedi Ohakim na jihar Imo ya bada labarin yadda shi da yaransa suka tsallake rijiya da baya a ranar Litinin.

Jaridar Daily Trust ta rahoto yadda aka halaka 'yan sanda yayin da miyagu suka kai farmaki kan tawagar motocin Ohakim a karamar hukumar Ehime Mbano dake Imo.

Tsohon gwamnan jihar Imo
Harin 'Yan Bindiga: Yadda ni da 'Ya'yana Muka Sha da Kyar, Tsohon Gwamna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A wata tattaunawa da TheNiche, wani dandalin yanar gizo, tsohon gwamnan yace motarsu da bata jin harsashi ce ta kare su. Ya labarta cewa:

Kara karanta wannan

Bidiyon Matar Aure Tana Gaggawar Ba Miji Abinci a Baki Kada ya Makara Aiki ya Janyo Cece-kuce

"Muna tuki tsakanin Isiala Mbano da Ehime Mbano. Wadannan mutanen sun rufe mu a wani wuri da ake kira Umualumaku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sun kawo mana hari ta baya kuma suka dinga harbin motocinmu babu sassautawa. A tunanina na mutu kuma tare nake da yara na biyu, daya mace, sai namiji.
"Abinda ya tsare mu shi ne motar mu da bata jin harsashi. Rayuwata a yau ita ce babbar baiwar da Allah yayi min tare da mota ta bata jin harsashi.
"Amma abun takaici ne yadda suka halaka yara na biyu har da direba. Tabbas, yara hudu muka rasa kuma ina takaici. Ta yaya haka zata faru? Wanne laifi suka yi?"

Ohakim yace bayan direbansa ya tsere daga inda lamarin ke faruwa, miyagun sun bi motar tare da cigaba da harbi.

"Sun bi mu tare da cigaba da harbin tayoyin mu. Cike da sa'a, babu iska a tayoyin amma mun cigaba da tafiya. Ko bayan da suka harbi tayoyin don hana mu tafiya, ba tayoyi gama-gari bane kuma basu tsaya ba. Da sai su ritsa mu tare da gamawa da mu.

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Fitaccen Sarki a Arewa, Sun Tafka Ta'asa

"Amma haka muka cigaba har muka isa gida. Mun tuka har kusan tsawon mintuna 20 kafin mu kai gida. Wannan ya tseratar da mu."

- Yace.

"Direban ya bayyana kwarewarsa a tuki har sai da muka rabu da su a wata iyaka inda ya shiga dama sai basu lura da inda ya bi ba, suka kama dayar hanyar zuwa Umuahia.
"Daga nan mun juya tare da komawa gida na. Sai gwamnatin Imo ta karo jami'an tsaro daga Owerri wadanda suka kawo min gawawwakin masu tsaro na.
“Dole in ce wannan ya zarce 'yan awaren IPOB. Wadannan kwararru ne, kuma horarru. Ba gama-gari bane. Suna tuki ne a BMW 5-Serie kalar bula kuma sabuwa dal. Sun zo halaka ni ne."

- Ya kara da cewa.

Kada ku bar Najeriya hannun 'yan ta'adda, Gwamna Ortom

A wani labari na daban, Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya yi kira ga hukumomin tsaro da kada su bar Najeriya a hannun miyagun 'yan ta'adda.

Yace Najeriya na bukatar zaman lumana da lafiya don haka kamata yayi 'yan kasa su bada gudumawar hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel