'Yan Najeriya Sun Zo da Sabon Salo, Suna Ta Wanke Sabbin Naira Don Gwada Ingancinsu
- ‘Yan Najeriya sun tsiri wani sabon salon kalubale a kafar sada zumunta don gwada ingancin sabbin Naira da aka buga
- Wannan na zuwa ne bayan da wani bidiyo ya yadu na yadda sabbin kudin ke zuba yayin da aka tsoma su a ruwa
- Mutane da yawa sun yi martani ta hanyar yada bidiyon yadda nasu kudin ya kasance; yana zubewa ko a’a
Najeriya - Biyo bayan wani bidiyon da wata mata Chinazo a kafar Twitter ta yada, inda tace kudin Najeriya sun wanke tas bayan jikewa a ruwa, ‘yan kasar da dama sun yi sabbin bidiyo sun yada a intanet.
A bidiyon da ta yada, ta ce ‘yar uwarta ta wanke gudan N500 a aljihi cikin rashin sani, wannan yasa sabon kudin ya sauya zuwa farar takarda.
Wannan lamari dai ya dauki dumi a kafar Twitter, domin kuwa mutane da yawa sun shiga mamakin yadda kudi zan kasance haka.
A bangare guda, ‘yan kasar da dama na tambayar inganci da gaskiyar abin da matar ta yada a Twitter.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
‘Yan Najeriya na gwada ingancin sabbin Naira
Ikrarin da Chinazo ya kawo wani sabon salo a kafar sanda zumunta, mutane suka fara jikawa tare da wanke sabbin kudin ganin ko da gaske suna zuba.
Sai dai, Dr Joe Aba, wata daraktar kasa a jami’ar DAI. DAIMaastricht ya yi tsokaci tare da wani gwaji a martani ga bidiyin Chinazo.
A cewar @DrJoeAbah, tabbas zubewar sabbin kudin Naira ba gaskiya bane, sai dai idan akwai wani lauje a cikin nadi.
A cewarsa:
“Na goga sabuwar N500 da ruwa da kuma auduga. A’a, launin bai wanke ba. Watakila matsalar a jikin gudan sabuwar N1,000 ne, wanda ni ban gwada ba. Sabuwar N500 dai a wuri na bata wata matsala. Zan gwada a injin wanki sannan na ba ku rahoto daga baya.”
Another video from @__bellefille also denied the claim that the new naira notes fade colour.
Har ila yau, @__bellefille ta karyata labarin cewa da gaske sabbin kudin Najeriya na zubewa idan suka jike.
Ta yada sabon bidiyo tare da cewa:
"Ga mutanen da ke cewa wai sabbin kudade na zubewa, meye-meye-meye."
A tun farko, Chinazo ta ce 'yar uwarta ce ta wanke N500 cikin kuskure, hakan ya maida sabon kudin zuwa farar takarda tas.
Asali: Legit.ng