Yunkurin tsige Buhari da Tirka-Tirka 10 da Aka Yi a Majalisar Tarayya a Shekarar 2022

Yunkurin tsige Buhari da Tirka-Tirka 10 da Aka Yi a Majalisar Tarayya a Shekarar 2022

Abuja - Abubuwa da-dama sun faru a majalisar wakilan tarayya da ta dattawa a shekarar bara, wannan rahoto ya tattaro wasu daga cikin manyansu.

1. Sabani a kan dokar zabe

An yi ta kai-komo tsakanin majalisa da bangaren zartarwa a kan dokar zabe, inda ‘yan majalisa su ka dage a kan wajibincin amfani da tsarin kato bayan kato wajen fito da ‘dan takara.

A farkon shekara aka yi garambawul ga sashe na 84 da ya hana masu rike da mukamai shiga takara.

2. Zaben tsaida gwani

Rahoton Daily Trust ya ce mafi yawan ‘yan majalisa sun nemi tikiti domin su zarce a 2023, amma da yawa ba za su dawo ba, daga cikinsu har da shugaban majalisar dattawa, Dr. Ahmad Lawan.

3. Tsige shugaban kasa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Kada Ku Bar Najeriya a Hannun ‘Yan Ta’adda, Gwamnan Binuwai Ya Roki Jami’an Tsar

Daga nan kuma sai aka ji ‘yan majalisa sun bada wa’adin makonni shida a kawo karshen rashin tsaro, idan ba haka ba suka ce za su tsige shugaban kasa, a karshe dai hakan bai yiwu ba.

4. Cushe a kundin kasafin kudi

Jaridar The Cable ta rahoto cewa a shekarar bara, zargin yin cushen biliyoyi a cikin kasafin kudin NUC, ma’aikatun tsaro, lantarki da na jin kai ya jawo surutu a zauren majalisar tarayya.

5. Tsarin mulkin kasa

Har ila yau, ‘yan majalisa sun yi kokarin yi wa tsarin mulkin kasa garambawul kamar yadda aka saba. Amma ‘yan majalsar sun zargi Gwamnonin jihohi da hana ruwa gudu wajen aikin.

Majalisa
Zaman karshe na Majalisar Tarayya a 2022 Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

6. Akawun majalisa

A shekarar nan, an dauki tsawon lokaci ana rigima a kan kujerar Akawun majalisa tsakanin Sani Magaji Tambuwal da Amos Olatunde Ojo wanda ya kamata ya yi ritaya a farkon bana.

7. Majalisa da Gwamnan CBN

Gwamnan babban banki ya ga ta kan sa a dalilin kawo dokar takaita kudi da canjin takardun Naira. Wannan ya sa ‘yan majalisar kasar suka gayyaci Godwin Emefiele domin ya yi masu bayani.

Kara karanta wannan

Shekarar 2022 Ta Zama Shekarar Zulumi Da Fargaba, Akalla Mutum 8,000 Ne Suka Rasa Ransu a Shekarar

Kudirorin da suka tada kura

8. Kudirin ruwa

Rahotannin sun nuna a cikin kudirorin da suka jawo abin magana akwai kudirin albarkatun ruwa da Hon. Sada Soli ya dawo da shi. A shekarar 2020, an yi fatali da wannan kudiri daga majalisar Najeriya.

9. Kudirin mata da shigan maza

Hon. Muda Lawal ya kawo kudirin da zai haramta yin shiga ta kishiyar jinsi. Daga baya an ki amincewa da kudirin domin akwai al’adar da aka san maza da daura zani ko makamantansu a wasu yankuna.

10. Kudirin da zai ba mata karfi

A 2022 aka kawo kudirin da ya nemi ya kara yawan kujerun mata a majalisa, ya kuma ware masu 20% a FEC da SEC tare da ba su damar zama ‘yan jihohin mazajensu, kudirin bai samu shiga ba.

Obasanjo a kan takarar Tinubu, Atiku, Kwankwaso

An ji labari, a matsayinsa na wanda ya yi aiki da duk manyan ‘yan takarar Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo ya bada ma’aunin da za ayi amfani da shi.

Kara karanta wannan

Kila CBN Ya Canza Shawara, Sanatoci Sun Ce a Ajiye Batun Canjin Kudi Sai Yunin 2023

Obasanjo yana ganin a cikin Tinubu, Atiku da Kwankwaso, babu mai abin-a-nuna, manufofi, halayen kwarai da lafiyar da zai mulki Najeriya irin Peter Obi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng