Amarya Ta Shafe Ango a Gaban Jama’a, Ya Ciro Daloli Ya Dankara Mata Jaka

Amarya Ta Shafe Ango a Gaban Jama’a, Ya Ciro Daloli Ya Dankara Mata Jaka

  • Wani bidiyo ya nuna lokacin amarya ke shafa kirjin ango a wurin taron biki saboda ya kira ta zai bata kudi, mutane sun girgiza
  • Yayin da ta durkusa a gabansa, angon ya sauya shawari, ya dauko makudan kudade ya zuba a jakar amaryar
  • Mutane da yawa da suka ga wannan bidiyo sun yi martani, sun ce ta tabo inda ya dace a jikin mijinta halali

Wani bidiyon da @oppyjay_alaga ya yada ya nuna lokacin da amarya ta gamu da ango cikin farin ciki a wurin biki, ango ya jika ta da kudaden kasar waje.

A lokacin wani taron gargajiya, amaryar ta durkusa a gaban angonta dauke da jaka yayin da MC ke rera waka.

A bidiyon da aka yada, an ga lokacin da ta matso, ta kama kirjin ango tana shafawa, hakan ya ba shi annashuwa.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Ta Shiga Aikin Soja, Hotunan Sauyawarta Sun Yadu

Amarya ta burge ango, ta shafa kirjinsa ya ba ta kudi
Amarya Ta Shafe Ango a Gaban Jama’a, Ya Ciro Daloli Ya Dankara Mata Jaka | Hoto: TikTok/@oppyjay_alaga
Asali: UGC

Yayin da take shafa shi, angon ya fasa ba ta kudi kadan da ya yi niyya tun farko, sai kawai ya cusa hannu a aljihu ya kwaso kudaden kasar waje masu yawa ya saka a jakarta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kirga kudin a gaban amaryar yayin da ita kuwa take ta murmushi. Mutane da yawa suka ce wannan amarya ta san hannunta.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Ga kadan daga abin da jama’a ke cewa game da wannan lamari da ya dauki hankalin ‘yan soshial midiya.

Awoyemi Balikees:

"Wannan amaryar ba ta wasa ko kadan.”

Celine dion:

"Mai daukar hoto na shirya fashi a gaba.”

OZ x:

"Kar dai Dala da Fam din Burtaniya nake gani? Anti, meye kika saka a jikinki.”

Adeline_0023:

"Mai daukar hoto mamaki yake wani tsafin wannan matar ta yi amfani dashi.”

Akleh_skin:

"Wannan shine ake kira ATM na gaske....wow.”

Kara karanta wannan

Kwana ta kwanaye: Bidiyon 'yar Arewa ya girgiza intanet, ta taka leda fiye da yadda maza ke yi

lily:

"Mai daukar hoto sai kallon gefe da gefe yake, ku dai ga abin da nake gani.”

Rita Micheal611:

"Mu mata da batun kudi, daidai yake da lamba biyar da shida.”

Bayan Kowa Ya Yi Ankon N150k, an Nemi Amarya a Ranar Aurenta an Rasa, Jama’a Sun Girgiza

A wani labarin kuma, amarya ta ba da kunya yayin da aka neme ta aka rasa a daidai lokacin da za adaura aure.

Kowa ya taru, ya yi ankon N150K, amma babu wanda ya ga inda amarya ta shiga, ango ya shiga damuwa.

Jama'ar kafar sada zumunta sun shiga mamakin wannan lamari mai daukar hankali, sun yi martani da yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.