Hotunan Yadda Dalibin Jami'a Ya Kirkiri Motar Daukar Kaya Da N1.2m a Matsayin 'Project'

Hotunan Yadda Dalibin Jami'a Ya Kirkiri Motar Daukar Kaya Da N1.2m a Matsayin 'Project'

  • Wani hazikin matashi dan Najeriya mai suna Eghosa Igbinosa ya kera wata motar daukar kaya a matsayin 'project' dinsa na jami'a
  • An gano Igbinosa wanda ya kasance dalibi a jami'ar Benin tsaye a kusa da motar daukar kayan wanda aka kera ta da shi na cikin gida ne
  • Ya ce ya kashe kudi naira miliyan 1.2 wajen cimma nasarar kera motar koda dai ya ce yana kan kera wata motar

Wani dalibin jami'ar Benin ya nuna fasaha mai ban mamakin yayin da ya kera wata motar daukar kaya a matsayin 'project' dinsa na jami'a.

Dalibin mai suna Eghosa Igbinosa ya ce ya yanke shawarar shiga wannan aiki ne saboda akwai bukatar motocin daukar kaya da dama a Najeriya.

Mota da matashi
Ribar Boko: Hotunan Yadda Dalibin Jami'a Ya Kirkiri Motar Daukar Kaya Da N1.2m a Matsayin 'Project' Hoto: Daily Trust Newspaper.
Asali: UGC

Igninosa wanda ya kasance dalibin PhD ya ce ya kashe kudi naira miliyan 1.2 don cimma wannan nasara da ya samu.

Kara karanta wannan

Duniya ta daina min dadi: Attajiri Dantata ya fada, ya bayyana abin da ya sauya masa a rayuwa

Dalibin UNIBEN ya baje kolin motar daukar kaya da ya kera

A wata hira da jaridar Daily Trust, Igbonosa ya koka cewa yana da matsaloli na kudi amma ya samu nasarar shawo kansu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Manyan matsalolin sune kudi da kayan aiki don kera jikin, amma mun cimma hakan ta hanyar amfani da kayan da ke nan."

Igbinosa ya bayyana a hirar da aka yi da shi cewa kaso 80 cikin dari na kayan da ya yi amfani da su an samo su ne a gida.

Ya fada ma Daily Trust cewa:

"Da ace kamfanin Ajaokuta da Alaja steel na aiki da ya taimaka sosai wajen kera jikin motar, saboda kaso 80 cikin dari na abun da aka yi amfani da shi daga gida ne, yayin da kaso 20 suka kasance daga jikin motocin da aka riga aka kera kamar su injin."

Kara karanta wannan

Ta gudu ta barni: Dan acaba mai yawo da jariri a cikin riga ya fadi tarihinsa mai ban tausayi

Ya yi kira ga gwamnati da ta hada kai da shi don ci gaba da bunkasa motar.

Daga tallan tuwa, yar Najeriya ta koma turai da zama tare da mijinta

A wani labarin, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wata matashiya da ke tallan tuwon rogo ta garzaya soshiyal midiya don nuna irin sauyin da Allah ya kawo mata a rayuwa.

A yanzu dai Allah ya tarbawa garin matashiyar nono inda suka koma turai da zama tare da mijinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel