Yan Ta'adda Masu Yawa Sun Sheka Barzahu Yayin Da Boko Haram Da ISWAP Suka Yi Musayar Wuta Na Awa 14

Yan Ta'adda Masu Yawa Sun Sheka Barzahu Yayin Da Boko Haram Da ISWAP Suka Yi Musayar Wuta Na Awa 14

  • Rikici tsakanin kungiyoyin ta'addanci na ISWAP da Boko Haram na kara kazanta yayin da kwandojin Boko Haram suka kai hari sansanin ISWAP
  • Rahotanni ya nuna cewa Abu Umaimah ko Bakoura Doro ne suka jagoranci mayakansu kai hari sansanin ISWAP a Tumbun Allura
  • Majiyoyi na bayyana sirri sun rahoto cewa an rika jin karar harba manyan bindiga sun daga yammacin Juma'a har Asubahin ranar Asabar

Jihar Borno - A wani abu mai kama da tabarbarewar yakin kin juna, an yi musayar wuta tsakanin mayakan Boko Haram da ISWAP na kusan awa 14 har zuwa ranar Juma'a.

Majiyoyi masu masaniya kan lamarin sun sanar da cewa mayakan Boko Haram masu yawa karkashin jagorancin Abu Umaimah ko Bakoura Doro da wasu kwamandoji hudu sun kutsa sansanin ISWAP da ke Tumbum Allura a karamar hukumar Kangar da ke arewa maso gabashin Abadam, jihar Borno.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Wata Fitacciyar Jami'a a Najeriya Ya Mutu Ba Zato Ba Tsammani

Borno
Yan Ta'adda Masu Yawa Sun Sheka Barzahu Yayin Da Boko Haram Da ISWAP Suka Yi Musayar Wuta Na Awa 14. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi na tattara bayanan sirri sun fada wa Zagazola, kwararre a bangaren nazarin yaki da ta'addanci a Tafkin Chadi cewa fadan da aka fara tun misalin karfe 4 na yammacin Juma'a har zuwa 5 na asubahin Asabar ya yi sanadin mutuwar mayaka da dama a bangarorin biyu.

Daya daga cikin majiyoyin ta ce:

"Muna ta jin karar harbin manyan bindigu sun jiya daga yankin Kangar.
"Akwai karar harbin manyan bindigu tun misalin karfe 5 na asubahi da ke cigaba babu kakkautawa."

Ya ce bayan nasarar cin galaba kan mayakan na ISWAP, Doro daga bisani ya janye dakarunsa ya nufi sansaninsa da ke Lele Karya kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Bidiyon arangama tsakanin mayakan ISWAP da Boko Haram a Borno

A baya-bayan nan, rahoto ya fito da ke nuna cewa mayakan kungiyar ISWAP sun kashe mayakan Boko Haram takwas yayin wata arangama da suka yi a Borno.

Kara karanta wannan

Kwankwaso a Gusau Jihar Zamfara: Zan Ba Da Fifiko Kan Muhimman Abubuwa 2 Idan Na Ci Zaben 2023

Zagazola Makama ya rahoto cewa kungiyoyin biyu sun yi bata-kashi a ranar Alhamis ne kusa da Krinowa da ke Marte.

Rahotanni sun nuna cewa kungiyar ISWAP ce ta kaddamar da harin kwantan baunar kan mayakan Boko Haram.

Mayakan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram da suka tsira daga harin sun hada da Gani Gado, Abou Adam da Abou Abubakar. An rahoto cewa ISWAP ta kwace makamai masu dimbin yawa daga Boko Haram bayan harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164