Yan Ta'adda Sun Sace Limamin Da Ya Dade Yana Wa'azi Kan Ta'addanci A Zamfara

Yan Ta'adda Sun Sace Limamin Da Ya Dade Yana Wa'azi Kan Ta'addanci A Zamfara

  • Yan fashin daji a jihar Zamfara sun sace babban limamin garin Masama-Mudi a ranar Alhamis 29 ga watan Disamban 2022
  • Dan uwan limamin mai suna Mustapha Mohammed ya ce yan bindigan sun dade suna neman kama limamin saboda wa'azi kan ta'addan da yadade yana yi
  • Bayan limamin, yan bindigan sun kuma sace wata budurwa da ake daf da daura mata aure da kuma wasu manoma da ba a tabbatar da adadinsu ba

Jihar Zamfara - Wata tawagar yan ta'adda sun sace babban limamin kauyen Masama-Mudi da ke Zamfara, saboda wa'azi da ya ke yi game da yan ta'adda.

Lamarin ya faru ne a ranar 29 ga watan Disamban 2022, HumAngle ta rahoto.

Taswirar Jihar Zamfara
Yan Ta'adda Sun Sace Limamin Da Ya Dade Yana Wa'azi Kan Ta'addanci A Zamfara. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da motoci biyu suka yi karo, mutum 1 ya hallaka, yawa sun jikkata

Mustapha Mohammed, dan uwan limamin ya ce:

"Shekarun babban limamin 75 a duniya, kuma yana da matan aure uku da yara 23 da wasu da dama da ke karkashinsa."

Yan bindiga sun dade suna neman limamin saboda wa'azinsa kan ta'addanci

Ya kara bayani cewa kungiyoyin yan ta'adda sun dade suna neman kama malamin tun Satumban wannan shekarar, sakamakon yawan wa'azin da ya ke yi kan ta'addanci a yankin.

Akwai lokutan da ya ke tserewa daga gidansa saboda ya tsira daga sharrinsu, ya ce.

Amma, a ranar Alhamis, yan ta'addan sun kama limamin a Sabon Gari.

Yan bindigan sun kuma sace wasu manoma da wata amarya a garin.

Martanin yan sanda

Umar Modibbo Halilu, DPO na yan sandan hedwatan yan sanda da ke karamar hukumar Bukuyum, ya fada wa HumAngle cewa:

"Mun san da harin kuma a yanzu muna kokarin magance lamarin a Masama-Mudi.
"Duk da cewa ba mu kawar da yan bindiga baki daya ba a yankunan, kamar yadda za ka iya gani, mun rage abin sosai. Shi yasa a yanzu maharan a karamar hukumar Bukuyum, yakin sunkuru suke yi."

Kara karanta wannan

Saboda yawan ganganci: Za a haramtawa 'yan sandan Najeriya shan giya gaba daya

Ba wannan ne karon farko da yan bindiga ke sace limami a jihar ba. A ranar 2 ga watan Satumba, an sace wani limami tare da wasu masu ibada a masallacin Zugu.

An kama wani mutum a Abuja da ya halaka abokin aikinsa kan kudi

Yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama wani mutum dan shekara 63 mai suna Taiwo Ojo saboda zarginsa da kashe abokin aikinsa.

An rahoto cewa Ojo ya samu rashin jituwa da abokin aikinsa mai suna Philip Kura ne saboda wani kudi, daga nan ya dauki shebur ya buga masa a kai, ya kuma fadi matacce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164