Jami'an Tsaron Nigeria Sun Kama Yan Awaren IPOB Wanda Ake Zargin Sun Kashe Gulak

Jami'an Tsaron Nigeria Sun Kama Yan Awaren IPOB Wanda Ake Zargin Sun Kashe Gulak

  • Hare-haren 'yan awaren Biafra na kara 'kamari a jihohin kudu maso gabashin Nigeria da suka hada da jihar IMO, Abia, Akwa-Ibom da sauransu
  • Shekara kusan biyu da suka wuce aka kashe wani tsohon hadimi9n shugaban kasar Nigeria a hanyarsa ta zuwa Fili da tashin jirgi a Imo
  • A Jiya jami'an tsaron Nigeria suka bada shelar kama wanda ake zargi da kashe Hadimi, wanda suka ce yan awaren IPOB ne

Imo - Jami'an tsaron Nigeria a jihar Imo sun kama wani tsohon soja, kuma mai fada aji na biyu na kungiyarr 'yan awaren Biafra mai suna Nwagwu Chiwendu, a wajen jana'izar mahaifinsa a babban birnin jihar

Wata majiya ta shedawa jaridar Leadership tsohon sojan yayi ikirarin kashe shararren dan siysan nan na arewa Ahmed Gulak, kuma shi ke shirya kai hare-hare ofishin hukumomin zabe a jihar

Kara karanta wannan

Bayan Raba Gari da Atiku, Gwamnonin PDP 5 Zasu Gana da Ɗan Takarar da Suke Shirin Goyon Baya a 2023

Yaushe aka kashe Ahmed Gulak?

An kashe dan siyasar a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2021 a jihar Imo, akan hanyarsa da zuwa filin tashi da saukar jiragen jihar.

Waye Chiwedu

Wani bayani da jaridar Neptuneprime ta samu yace tsohon sojan mai lamba (13NA/70/9974) ya bar aikin soja tare da shiga aiyukan yan awaren IPOB a jihohin kudu masu gabas inda ya zama kwamanda mai kula da yan kungiyar wajen amfani da makamai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ahmed Gulak
Jami'an Tsaron Nigeria Sun Kama Yan Awaren IPOB Wanda Ake Zargin Sun Kashe Gulak Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Majiyar tace:

"Wannan sojan, ya shiga aiyukan 'yan awaren IPOB, sannan kuma ya kasance jigo a cikinsu wanda yake da alhakin kula da hoiar da 'ya'yan kungiya a bangaren amfani da makamai, hakan ya sa ya zama na biyu a kungiyar sabida muhimmancinsa."

Majiyar ta ce kafin barinsa aikin, yayi aiki da atisayen "Operation Hadin Kai" inda anan ne ya kara samun gogewa. Majiyar tace an kama shi ne lokacin da yake halartar jana'izar mahaifinsa.

Kara karanta wannan

Dan Sanda Ya Harbe Wata Lauya a Hanyarta Ta Dawowa Daga Coci a Ranar Kirsimeti

Waye Ya Kashe Gulak

Ya tabbatar da shi ya kashe shahrarren dan siyasar Ahmed Gulak, kuma ya tabbatar da yin garkuwa da wasu kwararrrun masana da akai garkuwa da su kwanaki akan hanyar Owerri zuwa Okigwe.

Chiwedu ya ce:

"Ni ne garkuwa da wasu masana da kashe 'yan sanda guda biyu da suke gadinsu, kuma nine na kashe sojan da suke tare da kona motarsu kirar Hilux. Nine nake da alhakin kai hare-hare ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta a fadin jihar nan."
"Harin da aka kai caji ofishin yan sanda kwanannan nine na shirya aka kaishi."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel