Ta Kagu a Daura: Amarya Ta Isa Wajen Aurenta Da Wuri, Bata Tarar Da Kowa Ba a Bidiyo

Ta Kagu a Daura: Amarya Ta Isa Wajen Aurenta Da Wuri, Bata Tarar Da Kowa Ba a Bidiyo

  • A rana mafi muhimmanci a rayuwarta, wata amarya yar Najeriya ta yi watsi da al'adar yan Afrika na rashin bin lokaci inda ta isa coci da wuri
  • Kasancewar babu wanda ya hallara, sai amaryar wacce ke sanye da rigarta na aure da kawayenta suka yi amfani da wannan damar
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun jinjinawa tsarin amaryar na aiki da lokaci, inda suka bayyana ta a matsayin amaryar Najeriya ta farko da ta yi aiki da lokaci

Ga mamakin mutane da dama, wata amarya yar Najeriya da kawayenta sun isa wajen daurin aurenta da wuri.

Wani bidiyo da amaryar ta wallafa da kanta ya nuno ta sanye da farar doguwar riga irin ta amare tare da kawayenta yayin da suke TikTok.

Amarya da kawayenta
Ta Kagu a Daura: Amarya Ta Isa Wajen Aurenta Da Wuri, Bata Tarar Da Kowa Ba a Bidiyo Hoto: TikTok/@queenhyacinth9
Asali: UGC

Yan matan sun cika da farin ciki yayin da suke gwangwajewa cikin tsari ba tare da damuwa da rashin mutane a wajen bikin ba.

Kara karanta wannan

Kyakkyawar Budurwa Ta Fada Tarkon Son Wani Boka, Ta Saki Zazzafan Bidiyonsu a Kogi

Jama'a sun taya amaryar murna a wannan babban rana a rayuwarta, inda da dama suka bayyana cewa wannan ne karon farko da suke ganin amarya na bin ka'idar lokaci a Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Ellamai❤ ta ce:

"Kun tabbata bata yi kuskuren zuwa wani dakin taro na daban ba? babu wanda zai fada mani cewa mata sun isa wajen taro da wuri na yarda."

Elizabeth Nkemakonam ta ce:

"Nima na iya coci da wuri a ranar aurena amma wajen shagalin biki, a'a."

user5731803821777 ta ce:

"Ke ce amaryar farko da na ga kin hallara kafin fasto da kansa, ina taya ki murna."

Sama Manda ta ce:

"Amarya ta farko da ta aikata haka. Jinjinaga ga wacce ta tsara bikinki, mai gyaran gashi da wacce ta yi maki kwalliya."

Kara karanta wannan

Budurwa Mai Tallan Tuwo a Najeriya Ta tsallake, Ta Tare Da Mijinta a Turai, Sun Bar Jama'a Baki Bude

sarah_jay25 ta ce:

"Kina farin cikin yin aure."

Budurwa ta ce bata yin auren bayan mahaifiyar saurayinta ta saka ta wanke-wanke

Wata budurwa mai suna Bolladeasy daga kasar Indonesiya ta hau sama ta duro ta ce bata yi da saurayinta bayan ta kai ziyara ga mahaifiyarsa a karon farko.

Da isarta gidan, mahaifiyar saurayin ta tambayeta ko ta iya abinci inda dole ta shiga ta taimaka mata a kicin, sai dai kuma bayan an gama ta kuma saka ta wanke-wanke lamarin da yasa ta datse soyayyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng