Mutum 1 Ya Mutu, 8 Sun Jikkata a Wani Hatsarin Mota da Aka Yi a Anambra
- An samu mummunan yanayi yayin da wani hadarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a jihar Ananmbra
- An ruwaito cewa, mutum takwasi sun jikkata ciki har da yara kanana, an ceto wasu mutane da yawa
- Ana yawan samun hadurra a titunan Najeriya, musamman a lokutan bukukuwa na Disamba da sauransu
Jihar Anambra - Wani direba ya rasa ransa, wasu takwas sun jikkata a wani mummunan hadarin motan da ya auku a mahadar Uko kusa babban titin Onitsha-Nteje-Awka a jihar Anambra.
Wata mota ce kirar Toyota/Hiace bas mai lamba JVR 616 XA ta kwasunci ne ta yi taho mu gama da wata ‘yar uwarta bas mai lamba JJJ 179 XS a ranar laraba, Punch ta ruwaito.
Motocin sun dauko mutum 14; maza hudu manya da mata shida manya kana da yara kanana maza da mata wadanda biyar daga cikinsu sun kubuta babu rauni.
A cewar wani ganau, daya daga tayun mota mai JVR 616 XA ce ta fita wanda ya kai ga karo da daya motar bas din da ke tafe.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hukuma ta tabbatar da faruwar hadarin
Mukaddashin kakakin hukumar kiyaye haddura, Margaret Onabe ta tabbatar da faruwar lamarn a cikin wata sanarwa da ta fitar a Anambra a madadin kwamandan hukumar, Adeoye Irelewuyi.
Onabe ta ce, wadanda hadarin ya rutsa dasu tuni aka yi gaggawar tafiya dasu asibitin Chief Odumegwu Ojukwu Teaching Hospital da ke Amaku, Awka.
Hakazalika, bayan tabbatar da direban ya mutu, an adana gawarsa a dakin ajiye gawarwaki na asibitin, rahoton People Gazette.
Ya kamata arage gudu
Ta kara da cewa, sauran wadanda suka ji kananan raunuka sun sami kulawa ta hanyar wanke raunukan ta taimakon malaman jinya a yankin Nteje.
A cewar sanarwar:
“Kwamandan yanki na jihar Anamra, Adeoye Irelewuyi ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu tare da yin addu’ar waraka ga wadanda suka jikkata.
“Ya kuma gargadi masu motoci da su guji gudun wuce misali da kuma tukin ganganci, musamman a lokutan bukukuwan kirsimeti da ake samun cunkoson ababen hawa, Ku yi tuki don kare rayuka a kan hanyoyinmu.”
A wani labarin kuma, 'yan sanda uku da wasu fararen hula biya suka rasu a hadarin motan da ya auku a jihar Neja duk dai a irin wadannan lokuta na kirsimeti.
Asali: Legit.ng