'Yan Bindiga Sun Kai Hari Caji Ofis, Sun Kone ta a Anambra
- Wasu hatsabiban da ba a san ko su waye ba sun yi dirar mikiya ofishin 'yan sandan karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra gami da banka mata wuta
- Lamarin ya auku ne a safiyar Laraba, wanda ya jefa mazauna yankin cikin rudani da tashin hankali tare da firgici
- Duk da har yanzu ba a san dalilin harin ba, amma ganau ya shaida yadda 'yan ta'addan suka iso ofishin da tarin yawansu, inda suka jefa abubuwa masu fashewar cikin ginin
Anambra - Wasu wadanda ba a san ko su waye ba sun kona ofishin 'yan sanda a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.
Lamarin, wanda ya auku a safiyar Laraba, ya tada hankula gami da janyo rudani a yankin Ihiala, jaridar Punch ta rahoto.
'Yan ta'addan da tarin yawansu sun yi dirar mikiya ofishin 'yan sandan tare da budewa jama'an anguwar wuta, inda suka firgita 'yan sandan dake aiki wadanda hakan yasa suka ranta a na kare, kafin bankawa ofishin wuta.
Har zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoton, babu wanda ya san dalilin yin hakan, sannan ba a tabbatar ko hatsabiban sun tafi da bindigun 'yan sandan ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ruwayar jaridar TheCable ta bayyana cewa, haka zalika, har yanzu ba a ji labarin wadanda lamarin ya ritsa dasu ba, sai dai an tattaro yadda aka bankawa ofishin 'yan sandan wuta gami da lalata duk wani abu da takardun ofishin dake ciki.
Kakakin 'yan sandan jihar Anambra, DSP Toochukwu Ikenga ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda.
A cewar Ikenga:
"Jami'anmu a safiyar yau 28 ga watan Disamba, 2022 sun kai samame ga wasu 'yan bindiga da suka kai hari ofishin 'yan sandan Ihiala gami da gano bindiga kirar AK47 guda daya da aka yi watsi da ita. 'Yan bindigan sun ranta a na kare daga wurin saboda irin luguden wutar da jami'an 'yan sandan suka yi musu, amma lamarin bai ritsa da kowa ba.
"Cikin rashin sa'a, abubuwan masu fashewar da 'yan bindiga suka jefa ofishin 'yan sandan ya fara ci da wuta gami da tarwatsa ginin.
"Ana cigaba da aiki a yankin, sannan za a sanar da cikakken bayani game da lamarin daga bisani."
'Yan bindiga sun farmaki caji ofis a Ondo
A wani labari na daban, wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari caji ofis a jihar Ondo.
Basu tsaya nan ba kadai, sun halaka wani jami'in 'dan sanda inda suka aika shi ga mahaliccinsa.
Asali: Legit.ng