Ni ba Safaya Taya Bane Kuma Bana Amalala: Kwankwaso Ya Zolayi Abokan Hamayyarsa
- Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi shagube ga abokan hamayyarsa da suke tseren neman kujerar shugaban kasa tare a 2023
- Kwankwaso wanda ke neman kujerar Buhari a karkashin inuwar jam'iyyar NNPP ya ce shine ya fi kowa cancanta cikin yan takarar shugaban kasa
- Tsohon gwamnan na Kano ya ce cikin yan takarar harda masu amalala suna jika wando sannan ya kira wani da safaya taya
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Sanata Rabiu Kwankwaso, ya yi ba'a ga manyan abokan hamayyarsa a babban zaben 2023.
Tsohon gwamnan jihar Kanon ya yi bayanin dalilin da yasa ya fi cancanta a zabe shi a matsayin shugaban kasar na gaba.
Sahara Reporters ta nakalto Kwankwaso yana cewa:
"Yakamata yan Najeriya su yi zabe cikin hikima a wannan karon, don kasar na bukatar wanda zai iya ceto ta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na yi aiki da ma'aikatar tsaro, na yi aiki a matsayin gwamnan jihar Kano sannan na wakilci Kano ta tsakiya a majalisar dattawa tsawon shekaru da cikakken ilimin sanin abun da muke bukata."
Ya kuma yi tinkawo da takardun karatunsa yayin da yake shagube ga yan takarar shugaban kasa na jam'iyyun All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu da People Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar.
Ya kara da cewa:
"Ni likitan boko ne, sabanin wani mai takardar sakandare ko takardar difloma. Ba na amalala, kuma ni ba safarar taya bane."
Ma'anar shaguben da Kwankwaso ya yi
Ma'anar safaya taya na iya zama shagube ga Atiku, wanda ya yi mataimakin shugaban kasa sau biyu. Yan siyasa da dama na yiwa safaya taya kallon abun kunya ciki kuma harda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ya fi a kira shi da abokin tuki.
Yanzu-Yanzu: Peter Obi Na Kan Gaba Wajen Nasara a Zaben 2023, Kwankwaso ne Kashin Bayan Binciken ANAP/POI
Musamman Kwankwaso ya shawarci Tinubu a watan Yuli da ya mayar da hankali wajen kula da lafiyarsa maimakon yakin neman zabe.
A watan Fabrairu, an gano wani bidiyo da ya nuno tufafin Tinubu a jike kuma hakan ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.
Tufafin dan takarar shugaban kasar na APC ya jike ta baya lokacin da ya tashi tsaye a fadar Awujale na kasar Ijebu.
Daga bisani, ministan cikin gida, Rauf Arebesola ya kara zafafa lamarin bayan ya ce sun fara fitsari a jikinsu.
Peoples Gazette ta kuma rahoto cewa a watan Satumba, wani hoton Tinubu sanye da abun fitsari ya bayyana lamarin da ya kara haddasa damuwa game da lafiyarsa gabannin zaben 2023.
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame ya ce ya koyi darasi sosai a zaman shekaru hudu da ya yi a gidan maza.
Nyame ya ce babban abun da ya kula da shi shine cewa tsarin shari'ar Najeriya na aiki ne a gida biyu, daya na yan gata dayan kuma na marasa galihu.
Asali: Legit.ng