Peter Obi Na Kan Gaba Wajen Nasara a Zaben 2023, Binciken ANAP/POI

Peter Obi Na Kan Gaba Wajen Nasara a Zaben 2023, Binciken ANAP/POI

  • Sabon bincike ya nuna Peter Obi zai lashe zaben shugaban kasa idan aka gudanar da zabe yau
  • Dan takarar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ne kashin baya cikin yan takara 4 dake kan gaba
  • Kungiyar ANAP/POI ta shahara da gudanar da irin wannan bincike kuma kowace shekara tana dai-dai
  • Tun shekarar 2011, wanda binciken ANAP yace zai lashe zaben ne ke nasara daga baya

Legas - Karo na biyu cikin watanni hudu, sabon binciken da aka gudanar a watan Disamba ya nuna cewa dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, na kan gaba wajen lashe zaben 2023.

Kungiyar gudanar da kuri'ar jin ra'ayi NOI ta gudanar tare da hadin kan gidauniyar ANAP karkashin jagorancin mammalakin bankin StanbicIBTC, Atedo Peterside, ta bayyana sakamakon binciken.

Atedo Peterside ya bayyana cewa Peter Obi na gaban Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC); Atiku Abubakar na Peoples Democratic Party (PDP) da Rabiu Kwankwaso na New Nigeria People’s Party (NNPP).

Kara karanta wannan

Wata Sabuwar Kungiya Mai Hatsari Ta Ɓullo A Najeriya, Shugaban NSCDC Ya Yi Gargaɗi

Peter
Peter Obi Na Kan Gaba Wajen Nasara a Zaben 2023, Binciken ANAP/POI Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan ne a hirar da ya gabatar ranar Laraba a shirin 'PoliticsToday' na tashar ChannelsTV kuma LegitHausa ta shaida.

Ya ce Kwankwaso ya farfado yanzu sabanin watanni hudu da suka gabata.

Peterside ya ce idan aka gudanar da zaben yau, Peter Obi zai lashe zaben na kuri'u 23%, Tinubu 13%, Atiku 10%, sannan Kwankwaso 2%.

Ya ce an yi amfani da hirar wayar tarho wajen jin ra'ayin mutane saboda kusan kowa ya mallaki wayar salula yanzu a Najeriya.

Ya ce a baya su kan tura ma'aikata gudanar da wannan bincike da kansu amma sun lura mutane sun fara tsoron bayyana ra'ayinsu.

Ya kara da cewa yunwa, talauci, rashin tsaro da wahala ya sa mutane sun fara fadin ra'ayoyinsu.

A cewarsa, matasa yanzu sun fusata kuma shirye suke su kada kuri'a sabanin zabukan shekarun baya.

Kara karanta wannan

Bude 'Border': Atiku ya fadi abin da zai yiwa iyakokin kasar nan idan ya gaji Buhari a 2023

Wannan shine karo na biyu da gidauniyar Anap za ta gudanar da wannan bincike a wannan shekarar.

Atiku ya bayyana abinda zai yi idan ya sake fadi a 2023

Alhaji Atiku Abubakar, ya yi takaran kujeran shugaban kasa sau biyar a rayuwarsa.

Wannan takarar da yake yi a 2023 ne na shida,

Asali: Legit.ng

Online view pixel