Zamfara: 'Yan Ta'adda Sun Halaka Mutum 32, Sun Sako Wasu 200

Zamfara: 'Yan Ta'adda Sun Halaka Mutum 32, Sun Sako Wasu 200

  • 'Yan bindiga sun aika a kalla mutane 32 barzahu tare da 'yin garkuwa da mutane 200 a yankin Mutumji na karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara
  • Hakan ya biyo bayan batan bindigun biyu daga cikin 'yan ta'addan bayan rasa rayukansu sanadin wani rikici tsakaninsu da wata tawagar 'yan bindiga kan budurwa
  • Wadanda suka samu 'yancinsu sun bayyana yadda suka biya N6 miliyan da alkawarin cikasa 24 miliyan daga baya

Zamfara - A kalla 32 cikin mutane 200 da aka yi garkuwa dasu daga anguwar Randa cikin karamar hukumar Maru na jihar Zamfara ne suka rasa rayukansu a hannun masu garkuwa da mutane.

Kauyen Randa
Zamfara: 'Yan Ta'adda Sun Halaka Mutum 32, Sun Sako Wasu 200. Hoto daga Premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sarkin Mutumji, Abdulkadir Abdullahi ne ya bayyanawa Premium Times a yammacin Litinin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Daga Shiga Motar Haya a Titi, An Halaka Matasa 3 Tare da Cire Sassan Jikinsu

Haka zalika, Abdullahi ya ce an saki sauran 200 da aka sace bayan biyan kudin fansa.

Premium Times sun ruwaito yadda 'yan ta'addan wadanda mabiyan gawurtaccen shugaban 'yan ta'addan nan, Lawalli Damina, suka sace gaba daya mazan yankin Randa saboda batan bindigunsu

An yi garkuwa dasu ne bayan musanta sanin inda bindigun biyu da suka bace a yankin suke.

An gano yadda bindigun suke mallakin mayaka biyu na shugaban 'yan ta'addan wadanda wasu tawagar 'yan bindiga suka halaka bayan sun yi rikici saboda budurwa a yankin.

Sai dai, Abdullahi ya ce an biya N6 miliyan ga 'yan ta'addan yayin da za a biya N24 miliyan daga baya bayan an saki wadanda aka yi garkuwan dasu kamar yadda aka yi alkawari.

"An saki kimanin mutane 200 bayan halaka 32. Wadanda suka samu 'yanci daga 'yan bindiga suna samun kulawa a asibitin Dansadau.
"Wadanda aka sakin sun bayyana yadda 'yan bindiga suka halaka wasu 'yan anguwarsu ko dai ta hanyar yankan rago ko kuma bindiga ko kuma soka musu wuka har lahira. Sun labarta yadda sauran suka mutu ta hanyar shi'dewa ko cutuka.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Fitaccen Malamin Arewa Ya Nemi Mutane Kar Su Zabi Wanda Zai Murkushe 'Yan Bindiga

"Wadanda suka samu 'yancinsunsuna samun kulawa a anguwar Dansadau, suna tsoron komawa anguwanninsu saboda sauran kudi N24 miliyan da basu gama biyan 'yan bindigan ba kuma mutane na tsoron kada su kara kai musu hari."

- A cewar sarkin anguwar.

Boko Haram Sun Halaka Makiyaya 17 a Borno

A wani labari na daban, miyagun 'yan ta'addan Boko Haram sun halaka maiyaya 17 a kauyen Airamne dake Mafa a jihar Borno.

An gano cewa, 'yan ta'addan sun fi karfin makiyayan da makamai wanda hakan yasa suka ci galaba a kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng