‘Danuwan Abduljabbar Kabara Ya Fadi Silar Yanke Hukuncin Kisa da Yadda Za a Kare
- Askia Kabara yana ganin sabanin Abduljabbar Kabara da Karibullah Kabara ya jefa shi a matsala
- Kanin malamin ya ce a dalilin siyasa aka zartar da hukuncin kisa a kan Sheikh Abduljabbar Kabara
- A hirar da aka yi da shi, ‘danuwan shehin ya zargi Karibullah Kabara da malamai da hada taron dangi
Kano - Askia Nasiru Kabara ya yi hira ta musamman da Punch a kan hukuncin da aka yankewa malamin. Wannan Bawan Allah kani ne ga Abduljabbar Nasiru Kabara.
A ra’ayin Askia Nasiru Kabara, sabanin siyasa da wasu mutane ne ya sa Alkali ya zartar da hukuncin kisa a kan shehin malamin, ba laifin da ake tuhumarsa da yi ba.
Wannan mutumi da aka yi hira da shi yana cikin ‘ya ya 35 da Sheikh Nasiru Kabara ya haifa a Duniya, ya ce ko kadan bai yi mamakin hukuncin da aka yanke a kotu ba.
"Ban yi mamaki ba lokacin da na ji hukuncin domin tun farko abin da muke sa rai daga gwamnatin jihar Kano kenan. Tun farko rashin adalci aka fara, kuma na san akwai boyayyar manufan da ake neman a cin ma."
- Askia Nasiru Kabara
Askia Nasiru Kabara ya nunawa ‘yan jarida cewa Gwamnan Kano ya na da sha’awar shari’ar, sannan ya roki kungiyoyin kare hakkin Bil Adama su sa baki, a ceci shehin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Za a saki Sheikh Abduljabbar Kabara
"Ba na kotu a lokacin da aka zartar da hukunci. Daga bakin mutane na ji da suka kira ni bayan nan. Na fauwalawa Allah SWT komai, kuma ina ta addua’a. Ina sa ran Ubangiji yana sauraronmu kuma a karshe za a sake shi.
Na tabbatar da cewa Abduljabbar bai da laifin zargin da ake yi masa na yin batanci ga Annabi SAW."
- Askia Nasiru Kabara
Meya kai maganar kotu?
"Zallar siyasa ce. Akwai mutane da yawa da ke da hannu. Abin ya biyo ta fuskoki dabam-dabam domin Sheikh Abduljabbar ya tara makiya da yawa. Abin ya fara ne daga cikin danginmu, musamman yayana.
Karibullah Nasir Kabara ne ya tara malamai domin su bata Sheikh Abduljabbar, aka kafa wata kungiya mai suna Maja. Daga nan suka je wajen Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, wanda take da matsala da shi.
Daga nan sai aka fara tsara yadda za a koyawa Sheikh Abduljabbar Kabara hankali."
- Askia Nasiru Kabara
Za ayi fatali da hukuncin kotun shari'a
‘Danuwan wannan fitaccen malami ya ce tun fil azal ya san wannan ne shirin da aka yi, amma ya ce da zarar an daukaka kara, za ayi fatali da hukuncin kotun shari’ar.
An rahoto Askia Kabara yana cewa tun da aka tsare shehin, aka keta masa alfarmar magana da wa’azi, alhali an bai aikata laifin batanci ga Manzon Allah (SAW) ba.
A hirar da aka yi da shi, ya ce yayansa ya fi kowa yawan malami a kasar nan, kuma da kisa na tasiri, da ba a san da irinsu Wahabiyawa (‘Yan Izala) da Ibn Tamiyyah ba.
Abin da malamai suke fada
Ku na da labari Majalisar Malaman Musulunci a Jihar Kano ta yaba hukuncin kisa ta hanyar rataya da wata Kotun Musulunci ta yanke a kan Abduljabbar Nasiru Kabara.
A wani rahoto, mun tattaro maku maganganun malaman Musulunci da ake ji da su a kan Hukuncin da aka yi wa Kabara wanda ake zargi da laifin cin mutuncin addini.
Asali: Legit.ng