Gwamnatin Buhari na Kokarin Dawo da Harajin da Isa Pantami Ya Hana a Kakaba a 2022
- Gwamnatin tarayya ta na la’akari da tsarin karbar haraji daga duk wani kamfanin sadarwa a Najeriya
- Maganar ta je gaban ‘yan majalisa domin a tattauna a kai, tsarin zai fara aiki a 2023 idan ta tabbata
- A lokacin da gwamnati tayi niyyar lafta harajin, Isa Ali Pantami ne ya bada shawarar ayi watsi da shi
Abuja - Gwamnatin tarayya ta na duba yiwuwar lafta haraji a kan harkokin sadarwa bayan an dakatar da maganar, hakan zai jawo yin waya ya kara tsada.
Wani rahoto da muka samu daga Punch a ranar Juma’a ya nuna gwamnatin tarayya ta sake bijiro da wannan batu domin a aiwatar da shi a shekarar 2023.
Wannan bayani na cikin wata takarda da aka gani da za a gayyaci mutane domin tattauna kudirin tattalin arzikin 2022 a zauren majalisar wakilan tarayya.
Kwamitin harkar tattalin arziki na majalisar tarayyar kasar ya fitar da wannan takarda.
Ta koma, ta leko...
An fahimci harajin sadarwar da aka dakatar a shekarar nan, yana iya komawa gaban ‘yan majalisar wakilan Najeriya a kokarin da ake yi na samun kudin shiga.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kwamitin harkar kudin ya ce zai zauna da al’umma domin jin ra’ayinsu a kan kudirin tattalin arziki na shekarar 2022, kuma za a tabo maganar harajin.
Daga cikin abin da takardar kudirin take cewa shi ne Najeriya za ta rika karbar haraji daga kamfanonin sadarwa a karkashin sashe na 13 na wannan doka.
Shugaban kasa ne yake da ikon yanke kason harajin da za a karba a wajen kamfanonin.
Rahoton ya ce kudirin ya nuna babban dalilin hakan shi ne ya taimaka wajen kara kudin shiga da harajin da gwamnatin tarayya za ta rika samu a shekara.
Nawa za a rika karba?
A takardar, ba ayi bayanin adadin harajin da za a rika yankawa kamfanonin sadarwar da ke kasar ba. A karshe dai za a tashi da biliyoyin kudi a asusu.
A watan Yulin 2022 da aka bijiro da tsarin, an yi niyyar karbar harajin 5% kamar yadda yake a kudirin tattalin arziki tun 2010, amma ba a iya aiwatar da shi ba.
Kafin ranar 21 ga kowane wata ya kamata kamfanoni su biya harajin. Ministan sadarwa, Isa Ali Pantami ne ya roki a hakura saboda farashin waya zai tashi.
Bashir Machina v Ahmad Lawan
Idan aka shiga siyasa, za a ji labari kwamitin yakin neman zaben Bashir Machina a APC, ya ce Dr. Ahmad Lawan yana cin amanar Bola Tinubu a takarar 2023.
Amma kakakin kwamitin takarar Tinubu, Festus Keyamo ya karyata zargin, ya ce Lawan ba zai taba yin watsi da ‘dan takaran APC saboda Atiku Abubakar ba.
Asali: Legit.ng