Ana Saura Watanni 5 ya Bar Ofis, Shugaba Buhari Ya Yi Sababbin Nade-naden Mukamai
- A lokacin da makon nan ke zuwa karshe, Muhammadu Buhari ya yi wasu nadin mukamai a BOI
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Shekarau Dauda Omar da Mabel Ndagi
- Shekarau Omar zai rike Darekta na sashen SME a bankin, Mabel Ndagi za ta canji Toyin Adeniji
Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da sake nada Shekarau Dauda Omar a matsayin Darekta a bankin masana’antu na kasa.
Mallam Shekarau Dauda Omar zai zarce a kan kujerar da yake kai a halin yanzu na Babban darekta na harkar kananan kasuwanci (SME) a bankin BOI.
Rahoton da Daily Independent ta fitar a safiyar Alhamis, 22 ga watan Disamba 2022, ya nuna Shekarau Omar zai sake shafe wasu shekaru hudu a ofis.
Wannan sanarwar ta fito ta ma’aikatar kasuwanci, masana’antu da zuba hannun jari ta kasa.
Ifedayo Sayo ya fitar da jawabi
Mai taimakawa Ministan kasuwanci, masana’antu da zuba hannun jari wajen yada labarai, Ifedayo Sayo ne ya fitar da jawabi a kan sake nada Omar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mista Sayo ya ce Shekarau Dauda Omar zai cigaba da aiki a matsayin Babban Darekta a bankin na BOI bayan cikar wa’adinsa na farko a shekarar 2023.
Omar zai bar ofis a 2027
Sai a ranar 5 ga watan Maris na 2027 Darektan zai bar ofis idan har ba a sauke shi daga kujerar ba. Saura watanni kimanin biyu ya cinye wa'din farko.
A jawabin da Ministan ya fitar dazu, ya ce Omar ya yi aiki tukuru a bankin, ya ce a dalilinsa ne aka samu cigaba sosai a bangaren kananan kasuwanci.
Mabel Ndagi ta zama ED a BOI
A daidai wannan lokaci ne kuma shugaban kasar ya amince a nada Mabel Ndagi a matsayin babbar Darekta. Rahoton ne duk ya kunshi wannan labari.
Misis Mabel Ndagi za ta fara wannan aiki a ranar 19 ga watan Maris 2022, inda za ta maye gurbin Toyin Adeniji wanda take shirin barin ofis a farkon badi.
Zuwa watan Maris na 2023, Toyin Adeniji za ta kammala duka wa’adinta biyu a bankin tarayyar, babu dama ta kara zarcewa a kan wannan kujerar.
Rahoton ya ce yanzu haka Ndagi ce Babbar Manaja a sashen yada labaran cikin gida da na waje na bankin BOI, tayi shekaru 16 tana aiki da bankin kasar.
Me ke hana Buhari yawon kamfe?
A jiya aka ji labari Muhammadu Buhari zai goyi bayan Bola Tinubu/Kashim Shettima sai inda karfinsa ya kare domin ‘dan takaran ya zama magajinsa.
Duk da alkawarin da ya yi wa ‘dan takaran shugaban kasar, Buhari ya ce mulkin Najeriya zai fi cin lokacinsa a kan yawon tallatawa jama'a Tinubu.
Asali: Legit.ng