Gwamna Ya Karawa Ma’aikatan Jiha Albashi da 10%, Ya Rabawa Kowa Goron Kirismeti

Gwamna Ya Karawa Ma’aikatan Jiha Albashi da 10%, Ya Rabawa Kowa Goron Kirismeti

A makon nan Gwamnatin jihar Anambra ta yi wa ma’aikatanta karin albashi domin su ji dadin aikinsu

Farfesa Chukwuma Charles Soludo ya bada sanarwar nan da ya ziyarci sakatariyar ma’aikatan jiha

Mai girma Gwamnan ya kuma bada kyautar N15, 000 ga ma’aikata domin su yi shagulgulan kirismeti

Anambra - A jihar Anambra, Chukwuma Charles Soludo ya kara albashin da ake biyan ma’aikatan gwamnati da 10% domin ganin an zaburar da su.

Vanguard a rahoton da ta fitar a ranar Talata 20 ga watan Disamba 2022, ta ce Gwamnan ya bada wannan sanarwa ne da ya ziyarci sakatariyar jihar.

A wajen bikin ranar aikin gwamnati na shekarar 2022 a garin Awka, Farfesa Chukwuma Charles Soludo ya sanar da yi wa ma’aikata karin albashi.

Bugu da kari, Mai girma Chukwuma Charles Soludo ya bada sanarwar raba kyautar N15, 000 ga duk wani ma’aikaci a matsayin kyautar bikin kirismeti.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Cigaba da Sakin Hannu, An Raba Kyautar Miliyoyi da Ya Je Kamfe a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu buhun shinkafa

Amma gwamnan ya ce wannan shekara ba za a samu buhunan shinkafar da aka saba rabawa ba.

Farfesa Chukwuma Charles Soludo
Gwamnan Anambra, Chukwuma Charles Soludo Hoto: @CCSoludo
Asali: Twitter

“Mun duba yadda ake raba shinkafar kirismeti a baya, mun fahimci ba za ta yiwu mu cigaba da wannan tsari ba.
Na fahimci gwamnatocin baya su na raba kilogram 25 na buhun shinkafa ga ma’aikata a lokacin bikin kirismeti.
Amma halin da ake a Najeriya ya yi kamari, kowa yana kokawa. Farashi yana tashi, sai na duba abin da ya fi dacewa."

- Farfesa Chukwuma Charles Soludo

Kasa babu kudi - Gwamna

The Nation ta rahoto Gwamnan yana kokawa da yadda buhun shinkafa ya haura N40, 000 a kasuwa, ya ce kudin ya fi karin albashin sabon ma’aikaci.

Farfesa Charles Soludo ya fadawa mutanensa su yi hakuri domin bukatun kashe kudi su na karuwa alhali abin da ke shigowa asusun jihar ba ya karuwa.

Kara karanta wannan

Dubbannin Malaman Makaranta a Arewa Sun Yunkuro, Sun Ayyana Wanda Zasu Goyi Baya a 2023

Gwamnan ya bayyana cewa tun watan Fubrairu, kamfanin NNPC bai sa komai cikin asusun hadaka ba, hakan yana nufin kason kudin jihohi ya yi kasa.

Domin ganin kudi sun shigo asusun jiha a 2023, Gwamna Soludo zai maida hankali wajen haraji kamar yadda gwamnatin jihar Legas take yi ta samu IGR.

Atiku ya je Katsina

An ji labari ‘Dan takaran PDP a 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bada gudumuwar Naira Miliyan 50 ga wadanda rashin tsaro ya shafa a jihar Katsina.

Atiku Abubakar ya bada N50m da aka yi ambaliya a Jigawa da Bayelsa, haka ya lale wadannan kudi da gobara ta yi barna a kasuwar Kano a kwanaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng