Kotu Taki Amincewa Da Bukatar DSS Na Kama Gwaman Babban Banki

Kotu Taki Amincewa Da Bukatar DSS Na Kama Gwaman Babban Banki

  • Kotu taki Amsar bukatar hukumar tsaron farin kaya na kama gwaman babban bankin Nigeria.
  • Alkalin yace hukumar tsaron na shirin yin amfani da umarnin kotu dan aikata ba dai-dai ba wajen kama gwamnan
  • Gwamnan babban bankin kasa dai na san suka bisa ga wasu tsare-tsare da gwamnan ya shigo da su wanda suka shafi kashe kudade.

Abuja: Wata babbar kotu mai zamanta a Abuja tayi watsi da bukatar da Hukumar tsaron farin kaya tayi na neman izinin kama gwamnan babban banki CBN.

Wani dan sanda ya bayyanawa Premium Times takardar rokon da neman izinin kama gwamnan bankin bisa ga laifin Harkarlar kudade, zamba cikin aminci da kuma dagula harkokin tattalin arzikin kasar nan.

Kunshin takardar mai dauke da lambar sheda wacce ake karanta ta a FHC/ABJ/CS/2255/2022 a ranar 7 ga watan Disambar nan, kan batun kama gwamnan CBN din.

Kara karanta wannan

Daraktan Yakin Neman Zaben Peter Obi Zaiyi Zabe A Kurkuki, Sakamakon Umarnin Kotu Na A Tsareshi

Gwamna
Kotu Taki Amincewa Da Bukatar DSS Na Kama Gwaman Babban Banki Hoto: Vanguard
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma alkalin kotun John Tsoho yaki bayar da bukatar yana mai cewa:

" Abubuwa da hukumar tsaron ta nema, bai kai a basu wannan hurumin ba, kuma abubuwan basu kai ace an kama gwamnan ba."
"Duk abinda kuka rubuta kun rubutasu ne bisa zargi da rashin tabbas, dan haka na hana wannan umarnin."

Alkalin ya ci gaba da cewa:

"Sunan wanda kuka rubuta bai nuna gwamnan babban bankin ƙasa CBN, ne ba ko kuma wani ne mai Sunan Godwin Emefele"

Jaridar Sahara Reporters tace dalilin da yasa hukumar tsaron farin kaya ta DSS, din suke neman kama babban bankin kasa shine zarginsa da kuke da hannu wajen daukar nauyin hanyoyin ta'addanci a Nigeria.

Karar mai sakin layi hudu, tayi bayanin dalilin da yasa su hukumar tsaron farin kaya ta DSS, din suke so su kama gwamnan babban bankin Godwin Emefele

Kara karanta wannan

Kudin makamai: Tashin hankali ga dan takarar shugaban kasa, kotu ta daure jigon kamfen dinsa

Shin DSS Na Da Hurumin Kama Emefele

Alkali kotun ya ce da umarnin kotu ko ba umarnin kotu, hukumar tsaron farin kaya ta DSS, na da hurumin kama gwaman, bisa irin zarge-zargen da suka rubuta suna tuhumarsa.

"Ni ina tunanin kawai suna son amfani da kotu ne dan gudanar da wani aikinsu na gangan" inji alkalin kotun
"A dalilin haka na hana wannan umarnin"

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel