Jirgin farko a duniya da ke amfani da iskar Hydrogen ya fara aiki a Ingila (Bidiyo)

Jirgin farko a duniya da ke amfani da iskar Hydrogen ya fara aiki a Ingila (Bidiyo)

- An kaddamar da jirgin sama na farko da ake tada shi da sinadarin Hydrogen, a ranar 24 ga watan Satumba

- Kamar yadda kamfanin suka ce, sun kirkiro jirgin ne don a huta da amfani da mai a injina

- Shugaban kamfanin, Val Miftakhov, ya ce suna fatan nan da shekaru 3 su fara siyar da jiragen

An kirkiri jirgin sama na farko a tarihi dake amfani da sinadarin Hydrogen kuma har an tashe shi a sararin samaniya.

Jaridar How Africa ta wallafa yadda aka kaddamar da wani jirgin sama mai amfani da sinadarin Hydrogen a ranar 24 ga watan Satumba, a sararin samaniya a Bedfordshire da ke Ingila.

Kamfanin ZeroAvia, sune suka fara kirkirar jiragen saman dake amfani da sinadarin Hydrogen don siyarwa a cikin shekaru 3.

Val Miftakhov, shugaban kamfanin yace yana fatan wadannan jiragen zasu maye gurbin jiragen sama dake amfani da mai.

Ya ce, "Muna kokarin ganin cewa mun maye gurbin injinan jiragen sama masu amfani da mai,da injinan hydrogen".

"Mun tabbatar da munyi wa jiragen tsari ta yadda ba za su bari sinadarin yana fita ba, sannan za'a samu damar cika wa da zarar ya kare," cewar sa.

KU KARANTA: Zan bai wa 'yan Najeriya kariya ba tare da duba banbancin jam'iyya ba - Buhari

Jirgin farko a duniya da ke amfani da iskar Hydrogen ya fara aiki a Ingila (Bidiyo)
Jirgin farko a duniya da ke amfani da iskar Hydrogen ya fara aiki a Ingila (Bidiyo). Hoto daga Telegraph
Source: UGC

KU KARANTA: Katsina da Zamfara: 'Yan bindiga 32 sun shiga hannu, an kashe 1 - DHQ

A wani labari na daban, hukumomin tsaro a kasar Rasha sun kama wani tsohon dan sanda dake daga hannu akan titi da ke ta tara al'umma yana ce musu shi Annabi isa ne ya dawo duniya.

Mutumin mai suna Sergie Torop, wanda mabiyansa suke kiran shi da suna Vissarion, ya kai shekaru 30 yanzu kenan yana jagorantar mutane kan wata akida a wata coci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel