Budurwa Mai Shekaru 29 Ta Lallasa ’Yan Bindiga Dake Rike da AK-47, Ta Kubutar da Mutum 3 Daga Hannunsu

Budurwa Mai Shekaru 29 Ta Lallasa ’Yan Bindiga Dake Rike da AK-47, Ta Kubutar da Mutum 3 Daga Hannunsu

  • Wata mata mai shekaru 29 ta ba da mamaki yayin da samu kwarin gwiwar lallasa 'yan bindiga tare da kwato bindiga
  • 'Yan sanda sun bayyana cewa, wannan budurwa ta kuma yi nasarar ceto mutum uku da 'yan bindigan suka sace
  • Ana yawan samun hare-haren 'yan bindiga a Najeriya, lamarin da ke kara kawo cikas ga zaman lafiyar kasar

Jos, jihar Filato - Wata mata mai shekaru 29, Miss Lucy Tapnang ta fatattaki tawagar wasu masu garkuwa da mutane, ta kwace makamin AK47 tare da kubutar da wasu mutum uku da tsagerun suka sace a karamar hukumar Barkin Ladi da ke jihar.

Jaridar Tribune Online ta ruwaito cewa, wannan batu na fitowa ne daga bakin mai magana da yawun 'yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, wanda ya shaidawa manema labarai yadda lamarin ya faru a Jos.

Kara karanta wannan

A zauna lafiya: Hotuna yadda wata mata Musulma ta raba kudi, abinci da atamfa ga kiristocin Kaduna

Ya ce lamarin ya faru ne a makon da ya gabata, ranar Talata 13 ga watan Disamba, da misalin karfe 8:30 na yamma yayin da 'yan bindiga suka tare motar matafiya.

Yadda budurwa ta lallasa 'yan bindiga, ta ceto wadanda aka sace
Budurwa Mai Shekaru 29 Ta Lallasa ’Yan Bindiga Dake Rike da AK-47, Ta Kubutar da Mutum 3 Daga Hannunsu | Hoto: Plateau state police command
Asali: Facebook

Yadda lamarin ya faru

A cewarsa, tsagerun sun tare wasu matafiya da suka nufi Abuja a motar haya a kusa da makarantar kimiya ta Kuru, a yankin K-Vom a karamar hukumar Jos ta Arewa,

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Biyo bayan samun wannan labarin, hukumar 'yan sanda ta tura jami'anta a zagayen jihar.
"A kokarin kwato wadanda aka sacen cikin koshin lafiya, kwamishinan 'yan sanda jihar Filato, Bartholomew N. Onyeka ya umarci dukkan jami'an ofishoshin yanki da su kakkabe dazukan da ke zagaye, kuma inda suke kulawa dashi.
"Yayin da suke aiki bisa umarnin, babban jami'in ofishin yanki na Barkin-Ladi, CSP Yusuf Data ya hada jami'ai zuwa dajin Kssa, inda ya suka yi arangama da masu garkuwa da mutane ta hanyar samun bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An yi jana'izar wasu ma'aurata da 'yan bindiga suka kashe bayan karbe kudin fansa N7.5m

"Ta hanyar jajirecewar daya daga cikin wadanda aka sace, wata mata mai suna Lucy Jeremiah Tapnang, ta nuna jarumta ta hanyar kalubalantar tsagerun tare da sanin an kawo musu dauki."

Ji nayi kawai na tunkare su, inji matar

Da take bayani bayan yin wannan aiki, Tapnang ya ce, tana cikin motan fasinja lokacin da aka sace su aka shige dasu daji, NewsPeak ta tattaro.

Ta kuma bayyana cewa, ta samu kwarin gwiwar tunkurara 'yan bindigan ne lokacin da ta ga alamar an kawo musu dauki.

A wani labarin kuma, kun ji yadda 'yan sanda suka kamo wani yaron da ake zargin ya zagi gwamnan jihar Yobe a Arewa maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.