An Binne Wasu Ma’aurata Da ’Yan Bindiga Suka Kashe Bayan Karbar Kudin Fansa N7.5m

An Binne Wasu Ma’aurata Da ’Yan Bindiga Suka Kashe Bayan Karbar Kudin Fansa N7.5m

  • An yi jana’izar wasu ma’aurata da suka mutu a hannun ‘yan bindiga bayan da aka biya makudan kudaden fansa
  • Majiya ta shaida cewa, ‘yan bindiga sun sace ma’auratan ne tare da karbar Naira miliyan 7.5 a matsayin fansa
  • Rahoton da muka samo ya bayyana yadda lamarin ya faru, da yadda aka gano gawarwakinsu a bakin hanya

Jihar Anambra - An yi jana’izar wasu ma’aurata da ‘yan bindiga suka kashe duk da biyan kudin fansa na makudan kudade a jihar Anambra.

Wasu tsagerun masu garkuwa da mutane sun sace miji, Mr Emmanuel Chukwuemeka mai shekaru 36 da matarsa Chinwendu Chukwuemeka mai shekaru 30 tare da kashe su ba gaira ba dalili.

Rahoton da muka samu daga jaridar Punch ya ce, an binne su ne a garinsu, Isiekwulu da ke yankin Ukpo na karamar hukumar Dunokofia a jihar Anambra ranar Alhamis da ta gabata.

Kara karanta wannan

Alhamdulillahi: 'Yan sanda sun kama wasu tsagerun masu garkuwa da mutane

An binne ma'auratan da suka mutu a hannun 'yan bindiga duk da biyan kudin fansa
An Binne Wasu Ma’aurata Da ’Yan Bindiga Suka Kashe Bayan Karbar Kudin Fansa N7.5m | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Bikin binne su da aka yi ya jefa al’ummar yankinsu cikin firgici da matukar jimamin wannan rashi na ma’aurata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sace su tare da kashe

A rahoton, an ce mata da mijin sun shiga hannun ‘yan bindiga ne yayin da suke kan hanyarsu da ta dawowa daga coci a yankin Uke da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar.

Hakazalika, an tattaro cewa, ma’auratan na tare da jariri mai watanni hudu lokacin da aka sace su, wanda aka ce sun bar shi a mota tare da tafiya da iyayen nasa, kafar labarai ta LindaIkeji ta tattaro.

Wata majiya ta bayyana cewa, ahalin ma’auratan sun tara N5m tare da ba ‘yan bindigan, amma suka raina kudin tare da neman kari.

Daga baya ahalin sun dauki tsawon lokaci kafin hada N2.5m bayan siyar da kadarori, suka ba ‘yan bindigan.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Sheke Tsohuwa Mai Shekaru 120 tare da Wasu 5

Bayan karbar kudi, sun kashe wayoyinsu

Bayan karbar kudin, an ce ‘yan bindigan sun kashe wayoyoyinsu, daga nan ba a sake samun labarin halin da ma’auratan ke ciki ba.

Bayan watanni biyu, mazauna yankin suka gano gawarwakin ma’auratan a gefen hanya a kusa da titin Uke-Nnobi da ke jihar, an daure su da sarkoki.

A makon da ya gabata ne aka kama wasu tsagerun 'yan bindiga da ake kyautata zaton suna garkuwa da mutane, rahoto ya bayana 'yan sanda suka yi fama dasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.