Mutane Da Yawa Sun Mutu Yayin da Jirgin Soji Ya Saki Bam a Kauyen Zamfara

Mutane Da Yawa Sun Mutu Yayin da Jirgin Soji Ya Saki Bam a Kauyen Zamfara

  • Jirgin rundunar sojin saman Najeriya ya tashi Bam a ƙauyen Mutumji, ƙaramar hukumar Maru, a jihar Zamfara
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa mafi yawan waɗanda suka mutu 'yan ta'adda ne amma lamarin ya shafi fararen hula
  • Bayanai sun nuna cewa akalla mutane 64 ne suka rasa rayukansu a samamen sojin bayan sun biyo 'yan fashin jeji

Zamfara - Aƙalla mutane 64 ne suka mutu a wani luguden wutan da Jirgin yakin Sojin Najeriya ya yi ranar Lahadi a ƙauyen Mutumji, ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Premium Times cewa mafi yawan mutanen da suka mutu 'yan ta'adda ne, wasu kuma fararen hula ne mazauna garin.

Jirgin sojin Najeriya.
Mutane Da Yawa Sun Mutu Yayin da Jirgin Soji Ya Saki Bam a Kauyen Zamfara Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Mutanen, da suka kunshi mata da ƙananan yara sun rasa rayuwarsu ne lokacin da Jirgin yakin ya tashi Bam a garin yayin da ya biyo 'yan bindigan da suka gudo bayan sun kai hari.

Kara karanta wannan

Qatar 2022: Jerin Yan Kwallo 4 Da Suka Samu Kyautar Lambar Yabo

A ranakun Asabar da Lahadi, rundunar Sojin saman Najeriya ta kai ɗauki kan kiran gaggawan da mutane suka yi bayan wasu yan bindiga sun kai faramki ƙauyukan Malele, Ruwan Tofa, da Yan-Awake a yankin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mazauna yankin sun tabbatar da cewa samamen sojin sama a kauyuka uku masu makwaftaka ya tilasta wa 'yan ta'addan guduwa zuwa garin Mutumji mafi kusa don neman mafaka.

Wani mazauni, Nuhu Dansadau, yace ruwan wutan sojojin sama a kauyen Mutumji ya shafi fararen hula da dama, aƙalla mutane 64 suka mutu, wasu 12 suka jikkata.

Ɗansadau, mamban ƙungiyar kare hakkin ɗan adam, yace mutanen da duka ji rauni an tafi da su Asibitin Gusau, babban birnin jihar Zamfara domin duba lafiyarsu.

Haka zalika, magajin garin Mutumji, Abdulkadir Abdullahi, yace lamarin abun takaici ne da damuwa, har yanzun ana cigaba da kokarin tattara adadin mamatan, kamar yadda Channels ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: Ƙasurgumin Ɗan Bindigan da Aka Fi Nema Ruwa a Jallo Ya Shiga Hannu

Yan Bindiga Sun Harbe Shahararren Lauya a Babban Birnin Wata Jaha

A wani labarin kuma wasu miyagun 'yan bindiga sun harbe fitaccen lauya kuma ma'aikacin gwamnati a jihar Anambra

A bayanan da wakilinmu na jihar ya tattara ya nuna cewa lamarin ya auku ne ranar Asabar a kan babban Titin Enugu zuwa Onitsha a ƙauyen Umunga.

An ce marigayi lauyan ya tsaya biyan bukata ne sa'ilin da maharan suka mamaye shi, a kokarin guje musu ne suka harbe shi a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262