Yanzu Yanzu: Wasu Yan Bindiga Da Ba a San Su Waye Ba Sun Bindige Shahararren Lauya a Jihar Anambra

Yanzu Yanzu: Wasu Yan Bindiga Da Ba a San Su Waye Ba Sun Bindige Shahararren Lauya a Jihar Anambra

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe wani shahararren lauya kuma ma'aikacin gwamnati a jihar Ebonyi
  • Lauyan na a hanyarsa ta tafiya daga Abakaliki zuwa Onitsha lokacin da ya hadu da ajalinsa
  • Rundunar yan sandan jihar Anambea ta ce bata riga ta samu cikakken bayani kan lamarin da ya afku a ranar Asabar, 17 ga Disamba ba

Ebonyi - Wasu yan bindiga da ba'a sani ba sun bindige wani kwamishina a majalisar dokokin juhae Ebonyi, Barista Leonard Chibuzor Alegu.

Wakilin Legit.ng a Anambra, Mokwugwo Solomon, ya rahoto cewa lamarin ya afku ne da a daren ranar Asabar, 17 ga watan Disamba, a hanyar babban titin Enugu-Onitsha da ke garin Umunga, karamar hukumar Oyi ta jihar Anambra.

Gwamna Soludo
Yanzu Yanzu: Wasu Yan Bindiga Da Ba a San Su Waye Ba Sun Bindige Shahararren Lauya a Jihar Anambra Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP
Asali: Getty Images

Wata majiya ta bayyana cewa marigayin na hanyar tafiya daga Abakaliki zuwa Onitsha don halartan taron suna lokacin da abun ya afku.

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: Ƙasurgumin Ɗan Bindigan da Aka Fi Nema Ruwa a Jallo Ya Shiga Hannu

An tattaro cewa marigayin ya tsaya kama ruwa ne lokacin da makasan suka far masa, sannan a lokacin da yake fafutukar guje masu, sai suka harbe ahi a ciki; yayin da makasan suka tsere da mota da wayarsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rundunar yan sanda ta yi martani

Kakakin rundunar yan sandan jihar Anambra, DSP Tochykwu Ikenga, bai tabbatar da lamarin ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

A halin da ake ciki, shugaban kungiyar lauyoyin Abakaliki, Barista Victor Alo, ya fada ma manema labaraj a waya cewa a gaggauta kai marigayin asibiti a Umudioka, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Alo, wanda ya shima lauya ne mazaunin Onitsha ya kuma ce an ajiye gawar mamacin a wajen ajiyan gawa na Awkuzu, yana mai cewa sun kai rahoton lamarin hedkwatar yan sanda na Oyi a Nteje.

Bata gari sun bankawa wata kotu wuta a jihar Imo

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Jama'a suna ta mutuwa bayan cin abinci mai guba a wata karamar hukuma

A wani labari na daban, wasu yan daba sun bankawa kotun majistare na Owerri, babban birnin jihar Imo wuta a ranar Lahadi, 18 ga watan Disamba.

Da take tabbatar da lamarin, rundunar yan sandan jihar Imo, ta ce tuni ta fara bincike cikin lamarin don kamo masu laifin tare da gurfanar da su a gaban doka don fuskantar hukuncin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel