Rundunar 'Yan Sanda Ta Kama Manajan Cibiyar Jarabawar JAMB, Na Shiyyar Kebbi

Rundunar 'Yan Sanda Ta Kama Manajan Cibiyar Jarabawar JAMB, Na Shiyyar Kebbi

  • Yan Sanda Ne a jihar kebbi suka gabatar da wani manajan cibiyar JAMB, a Jihar Kebbi kan zargin satar kwamfutoci
  • Ba wai iya satar ba, bayan satar ma ana zarginsa da saida kwamfuwotocin ga wani mai cibiyar rubuta jarabawa a jihar Sokoto
  • Kwamishinan yan sanda yace za'a dau mataki sosai dan magance wannan matsalar

Kebbi: ‘Yan sanda a jihar Kebbi sun kama wani Abubakar Ismail, manajan wata cibiya JAMB da ke Zuru a karamar hukumar Zuru a jihar Kebbi da laifin satar kwamfutocin cibiyar kirar HP, guda 83.

Yayin da ake holen mutumin ga manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Birnin Kebbi tare da wasu miyagu da aka kamasu tare, a gaban wakilin jaridar Leadership

kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmed Magaji Kontagora, ya ce manajan hukumar ta KEBNA ICT-JAMB, ne ya kai rahoton lamarin a sashin ‘yan sanda na Zuru.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Samu Gagarumin Tagomashi, Dubban Mutane Sun Sauya Sheka A Jihar Sokoto

Ya kara da cewa shugaban ya sanar da ’yan sanda cewa a lokacin da ya ziyarci cibiyar ya gano cewa wanda ake zargin wanda shi ne manajan shafin ya sayar da kwamfutocin cibiyar.

Post-JAMB
Rundunar 'Yan Sanda Ta Manajan Hukumar Shirya Jarabawa Shiga Jami'a JAMB, Na Shiyyar Kebbi Hoto: Guardian
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda 'yan sandan suka ce, ya siyarwa da Chikwudi Otutu, mai Otutu Computer Centre, Sokoto a Sokoto akan Naira 40,000 kan kowacce kwamfuwuta.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa, rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar kwato kwamfuwotoci 76 daga cikin kwamfutocin.

Inda ya ce wanda ake zargin da sauran wadanda aka kama za a gurfanar da su a gaban kotu domin gurfanar da su gaban kuliya.

Jaridar WithinNaija ta wallafa cewa, kwamishinan yan sandan jihar Kebbin Ahmed Magaji Kontagora yace zasu ci ngaba da bincike al'amarin.

Matsalar banzatan da kayan gwamnati dai ya zama wani ruwan dare da kowa kan iya yin yadda yaga dama dasu.

Kara karanta wannan

"Ku Taimaka Ku Zabi APC Sak a 2023" Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Roki 'Yan Najeriya

A misalce ina kwamfuwotocin da akai amfani da su a zaben 2007, da na 2011, amma ko a kasafin kudin da hukumar Zabe ta kare na shekarar bara saida tace zata siyo wasu kwamfowotocin.

An Duba Wasu Cibiyoyin Jarabawar JAMB, A Dutse

Ofishin hukumar JAMB, a jihar Jigawa ya duba cibiyoyi 14 na rubuta jarabawar a shirye-shiryen gudanar da jarrabawar ta shekarar 2023.

Jardiar Vanguard ta rawaito cewa jami’in hulda da jama’a na hukumar a jihar, Mukarram Bello, ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Dutse ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida