Majalisar Malaman Kano ta Fitar da Matsaya Kan Hukuncin Rataye Abduljabbar Kabara
- Majalisar malaman addinin Musulunci na Kano sun yaba da hukuncin Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola
- Alkali Ibrahim Sarki Yola ya samu Abduljabbar Nasiru Kabara da laifin batanci ga Annabin tsira SAW
- A wata sanarwa daga bakin Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, majalisar malaman jihar ta yaba da hukuncin
Kano - Shehunan jihar Kano ta karkashin Majalisar malaman addinin Musulunci, sun yi magana kan hukuncin da aka yi wa Abduljabbar Nasiru Kabara.
Aminiya ta ce Majalisar malaman ta fitar da sanarwa ta musamman ta bakin Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, tana mai yabawa hukuncin da Alkali ya zartar.
Sa’idu Ahmad Dukawa ya ce majalisar malaman tayi ta bibiyar duk zaman da ake yi a shari’ar, kuma ta gamsu da hukuncin da Alkali ya yi a ranar Alhamis.
Dr. Dukawa ya bayyana cewa abin da suke fata shi ne hukuncin ya zama darasi nan gaba ga duk wanda zai nemi ya yi batanci ga Annabi Muhammad SAW.
An yabawa Ibrahim Sarki Yola da Lauyoyi
A jawabin da aka fitar a ranar Juma’a, 16 ga watan Disamba 2022, majalisar malaman na jihar Kano sun mika godiyarsu ga shi Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton ya ce majalisar ta kuma yi godiya ta musamman ga Lauyan da ya tsayawa masu shigar da kara wajen ganin an hukunta Malam Abduljabbar Kabara.
A karshe, Dr. Dukawa a madadin majalisar malaman addinin Musulunci na jihar Kano, ya yabawa dukkanin wadanda suka taimaka wajen wannan kara.
An yi wa Abduljabbar Kabara adalci - Dukawa
A cewar malamin, kotu ta bada duk wata dama ga Sheikh Abduljabbar Kabara domin ya kare kansa daga zargin da ake yi masa na batanci ga Annabi SAW.
Dukawa ya ce a karshen zaman da aka yi a kotu, wannan malami bai iya kare kansa daga tuhuma ba, a karshe sai zargin yin batancin ya dawo kan wuyansa.
“Wannan hukunci, muna fata, zai zama izina ga sauran masu irin wannan akida.
“Wannan majalisa na mika godiya ta musamman ga Alkali Ibrahim Sarki Yola, lauyan masu gabatar da kara da kuma dukkanin bangarorin da suka tabbatar da cewa an yi abin da ya dace wajen yanke hukuncin da ya dace ga wanda ake tuhuma”.
- Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa
Akwai siyasa a lamarin - Maqari
A ranar da abin ya faru, an samu rahoto cewa Farfesa Ibrahim Maqari ya nuna banbamcin siyasa ne ya jawo aka yankewa malamin hukuncin rataya.
Limamin ya ce a tarihi, mafi yawan wadanda aka kashe da sunan zindiƙanci, ba shi ne asalin laifinsu ba, illa iyaka ana fakewa da wannan ne a ga bayansu.
Asali: Legit.ng