Ma’aikacin Banki Ko Mai Talla: Matashi Na Samun N20k Kullun Daga Siyar Da Alale Saboda Yanayin Shigarsa

Ma’aikacin Banki Ko Mai Talla: Matashi Na Samun N20k Kullun Daga Siyar Da Alale Saboda Yanayin Shigarsa

  • Wani matashi a jihar Uyo ya yi suna saboda yanayin shigar da yake yi yayin da yake tallan alalen ganye
  • Eteng wanda ya fito daga Uyo ya ce yana irin shigar da yake yi ne don jan hankalin kwastamomi su siya kayan shi
  • Ya ce daga abun da yake samu ne ya dauki dawainiyar kansa har ya kammala sakandare, ya kuma ce ya taba siyarwa wata kafin shima ya fara nasa na kansa

Akwa Ibom - Ba don farantin da ake gani a kansa ba, za a dauka wani ma'aikacin banki ne a daya daga cikin manyan bankunan Najeriya.

Eteng mai shekaru 24 daga Uyo a jihar Akwa Ibom ya kan sanya kwat da rigarsa mai kyau cike da tsafta yayin da yake zuwa aikin tallan alallen ganye.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Karamar Yarinya Ke Sharholiya Cikin Kaji Ya Dauki Hankali, Ta Zama Kamar Shugabarsu

Eteng yana talla
Ma’aikacin Banki Ko Mai Talla: Matashi Na Samun N20k Kullun Daga Siyar Da Alale Saboda Yanayin Shigarsa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yana nade alallen da kyau a ganye sannan ya zuba abin sa a faranti ya daura a kai yana siyarwa N100 kowane guda daya kuma yana siyar da N20,000.

Ya sauya daukar da ake yiwa masu irin sana'a tasa

Mutane da dama sun raina sana'ar sannan ba a ganin girman masu tallansa saboda yanayin shigarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma Moses Eteng ya siyawa kansa daraja ta yanayin shigar da yake yi.

Premium Times ta rahoto cewa Eteng ya zabi yin irin wannan shigar ne don jawo kwastamomi kuma ya fita daban cikin tarin masu talla da ke yawo a titin Uyo.

Eteng ya fada ma jaridar cewa domin samu kwatamomi, sai ya karanci mutane sannan ya fahimci abun da suke so.

Ya ce abun da yake yi yana burge mutane kuma masu talla da dama na son haka amma basa iyawa lamarin da yasa ya fita daban. A cewarsa, yana shiga don tallata hajarsa.

Kara karanta wannan

Dalibi Mai Sayar Biredi Ya Zama Babban Dan Kasuwa, Yana Samun N41.5m a Shekara

Ya ce duk wanda ya kalle shi zai fahimci cewa kayan da yake tallatawa sun yi kama da shi. Ya ce kyakkyawar shigarsa na bunkasa kasuwancinsa.

Eteng ya kuma samawa kansa suna a matsayin mai saida alale mai ilimi a tsakanin masu siyan kayansa.

Shi da kansa ya dauki nauyin karatunsa na sakandare kuma ya taya wata siyar da alale tsawon shekaru 10.

Zama dan kasuwa

Ya fara nasa sana'ar ne a 2018 bayan ya koma kauye lokacin da ya rabu da shugabarsa.

Mutumin da ya fito daga karamar hukumar Yankuur ya ce ya yiwa matar inda take matsa masa sannan da ya koma Uyo, sai ya fata siyar da nasa alalen.

A cewar Eteng, da wannan kasuwancin, ya yi nasarar daukar dawainiyar kansa a makarantar sakandare.

Eteng na bin ka'ida wajen tabbatar da ganin ya dafa alalensa cikin tsafta.

Matashi ya je hutu a Turai, Ya dawo ya tarar da aika-aika a gidansa

Kara karanta wannan

Ta yi daidai: Martanin jama'a yayin da magidanci ya dauko karuwa, ta saci kwal din N6m a gidan abokinsa

Wani matashi ya nuna bacin ransa a soshiyal midiya bayan ya je hutun makonni uku a Turai amma ya dawo ya tarar mai aikinsa ta yi masa aski.

Mai aikin kula da gidan nasa ta kwashe duk wasu nau'i na kayan abinci da ya tafi ya bari kuma ko da ya dawo bashi da ko sisi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel