Kai Abin Koyi Ne Ga Dimokradiyyar Afrika, Shugaba Biden Ya Yaba da Shugabancin Buhari

Kai Abin Koyi Ne Ga Dimokradiyyar Afrika, Shugaba Biden Ya Yaba da Shugabancin Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kalmomin yabo masu daukar hankali daga shugaban kasar Amurka
  • Joe Biden ya bayyana cewa, Buhari ya zama abin koyi ga kasashen Afrika idan ana maganar dimokradiyya
  • A bangare guda, shugaba Buhari ya yi martani, ya kuma yiwa Biden fatan alheri a zaben da za a gudanar a Amurka

FCT, Abuja - Shugaban kasa Amurka Joe Biden ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya bisa shayar da ‘yan Najeriya romon dimokradiyya da fadada dimokradiyar a Afrika.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar ta hannun mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu bayan ganawar Buhari da Biden a birnin Washington ranar Laraba.

Idan baku manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi kasar Amurka don halartar wani taron shugabannnin kasashen Afrika, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa za mu zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa – Kiristocin Kudu

Biden ya yaba Buhari, ya ce babu kamarsa a dimokradiyyar Afrika
Kai Abin Koyi Ne Ga Dimokradiyyar Afrika, Shugaba Biden Ya Yaba da Shugabancin Buhari | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Shugaban na Amurka ya ce, wannan taro Amurka ta hada shi domin tattaunawa da shugabannin Afrika kan lamurran da suka shafi alakarsu da kasar gabanin zaben da kasar za ta gudanar nan ba da dadewa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Na bibiyi Buhari kafin ya zama shugaban kasa, inji Joe Biden

Biden ya ce ya bibiyi tafarkin Buhari tun yana shugaban adawa har yazo ya zama shugaban kasa a Najeriya, ya gamsu da nagartarsa.

Ya kuma kara da cewa, abin a yaba ne yadda Najeriya ta zama abin kwatance a nahiyar Afrika wajen fadada tafarkin dimokradiyya, Vanguard ta ruwaito.

Ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda kin neman sauya dokar Najeriya tare da neman wa’adi na uku na shugabancin kasar nan.

Hakazalika, ya yabawa shugaban bisa ba hukumar zabe mai zaman kanta INEC damar yin ayyukanta yadda ya dace ba tare da wata tsangwama ba.

Kara karanta wannan

2023: Na Gode Allah da Tinubu Bai Zabe Ni a Matsayin Abokin Takara Ba, Tsohon shugaban Majalisa

Matsalolin kasashen Afrika

Biden ya kuma bayyana cewa, ya fahimci kalubalen da kasashen Afrika ke fuskanta, inda yace Amurka a shirye take ta tallafawa kasashen wajen warware duk wata matsala.

Da yake martani, shugaba Buhari ya bayyana godiya da yadda shugaban na Amurka ya yabe shi, kana ya yi masa fatan nasara a zaben da za a gudanar nan gaba a Amurka.

Ya kuma gode masa bisa shirya wannan babban taro mai tarihi da tasiri ga shugabannin na Afrika.

Tun farko Biden ya gayyaci shugabannin Afrika su zo don wannan zama mai muhimmanci, shugaba Buhari na daga cikin shugabanni sama da 40 da aka gayyata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel