Tare Suka Tashi: Bidiyon Karamar Yarinya Tana Rayuwa Cikin Kaji Ya Ba Da Mamaki, Suna Bibiyarta Kamar Mutane

Tare Suka Tashi: Bidiyon Karamar Yarinya Tana Rayuwa Cikin Kaji Ya Ba Da Mamaki, Suna Bibiyarta Kamar Mutane

  • Wani bidiyon karamar yarinya tana wasa a gonar iyayenta cike da kaji ba tare da tsoron komai ba ya haddasa cece-kuce
  • An gano yarinyar wacce ta taso kusa da gonar tare da sabawa da kajin tana tafiya a cikinsu inda suke take mata baya kamar wasu mutane
  • Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka ga bidiyon sun yi mamakin yadda yarinyar ta sake sosai a tsakanin manyan kaji

Wata mata mai suna @cyruschick wacce iyalinta suka mallaki gonar kaji ta saki bidiyon diyarta Kayden da yadda take wasa a cikin gonarsu tun tana yar karama.

A farkon bidiyon, an gano yarinyar zaune cikin daruruwan kaji yayin da suke yawonsu kewaye da ita. Ta kasance cikin walwata a tsakaninsu.

Yarinya da kaji
Tare Suka Tashi: Bidiyon Karamar Yarinya Tana Rayuwa Cikin Kaji Ya Ba Da Mamaki, Suna Bibiyarta Kamar Mutane Hoto: TikTok/@cyruschick
Asali: UGC

Kyakkyawar yarinya na wasa da kaji

An kuma gano Hayden wacce ke shekaru uku a yanzu tana tafiya a wani budadden waje yayin da manyan kaji ke take mata baya tamkar ita ce shugabar su.

Kara karanta wannan

Daga hannun PDP muka gaji matsalar Boko Haram : FG Ta Maidawa Atiku martani

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har kamo kaji yarinyar tayi ba tare da tsoro ba. Mutane da dama sun nuna sha'awarsu kan yadda ta sake sosai da dabbobin.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

whitney ta ce:

"Na kasa gane dalilin da yasa da shekaruna amma har yanzu ina tsoron rike kaza."

everything_8908 ta ce:

"Na so wannan kamar kajin sun girma ne tare da ita."

user8080155500720 ya ce:

'"Yadda nake tsoron kajin nan sannan ga karamar yarin a nan tana sharholiyarta, ina son zama kamar ita."

Penguin ya ce:

"Na girma a gonar kaji kamar haka. akwai dadi sosai."

Bidiyon jinjira yar kwana kwana daya da ta yi murtuk da fuska ya ba da mamaki

A wani labarin, mun ji cewa jama'a sun cika da mamaki bayan ganin bidiyon wata jinjira yar kwana daya da ta yi kicin-kicen da fuska sai ka ce hadarin kaji.

Kara karanta wannan

A Ranar Aure, Ango ya Fasa Bayan Gano Amarya ta Kaiwa Tsohon Saurayinta Ziyarar Bankwana

Mutane da dama da ke amfani da soshiyal midiyan sun yi martani a kan bidiyon, sun ce ga dukkan alamu yarinyar bata shirya fitowa nan duniya ba amma mahaifiyarta ta yi karanbanin sumbulota.

Tuni dai bidiyon ya shahara a shafukan soshiyal midiya musamman ma a dandalin TikTok.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng