Dan Takarar Jam'iyyar PDP Na Shugaban Kasa Yace Har Yanzu Yana Mamakin Cewa Akwai Boko Haram

Dan Takarar Jam'iyyar PDP Na Shugaban Kasa Yace Har Yanzu Yana Mamakin Cewa Akwai Boko Haram

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya zargi gwamnatin APC da jan kafa wajen magance matsalar tsaro a Nigeria
  • Atiku Abubakar yace bai ga dalilin da zai sa har yanzu ace akwai kungiyar ta'addanci ta Boko-Haram ba
  • Ministan labarai da al'adu ya maidawa dan takarar martani yana mai cewa, jam'iyyar sa ta PDP zai tuhuma game da wannan batun

Abuja: Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar yace bai fahimci lamarin boko haram ba, inda ya koka, yace duk da kokarin da sojoji sukeyi, ba’a kawar da ta’addacin ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ya bayyana hakan ne a Lahadin nan data gabata yayin wani taron jin ta bakin yan takara da aka gabatar a gidan Talabijin na Channels TV.

Kara karanta wannan

2023: Babu Wata Matsala Tsakani Na Da Atiku, Gwamna Wike Ya Faɗi Inda Matsalar Take a PDP

Atiku wanda yake amsa tambayoyi kan rashin tsaro, inda aka tambayeshi matsayinsa kan boko haram, yace:

“Har yanzu na kasa gane dalilin da ya sa za'a ce akwai boko haram. Kaga na yi aiki a yankin arewa maso gabas, kum a matsayin kwastam, na yi sintiri a yankin arewa maso-gabas gaba dayanta, don haka ina da masaniyar kan yankuna iyaka. Har yanzu ban ban ga wajen da za'a ace an buya da za'a ce ba'a ganin wanda ya buya din ba."

Atiku Tinubu
Dan Takarar Jam'iyyar PDP Na Shugaban Kasa Yace Har Yanzu Yana Mamakin Cewa Akwai Boko Haram
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Martanin Ministan

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Muhammad, ya caccaki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da cewa bai fahimci lamarin Boko Haram ba, yana mai cewa jam’iyyarsa ce ta dagula lamarin.

Ya ce bai kamata tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wannan kalamin ba, domin a karkashin mulkin jam’iyyarsa ne aka fara rikicin Boko Haram a shekarar 2009.

Kara karanta wannan

Kowa ya huta: Atiku ya fadi yadda zai yi kungiyar ASUU idan ya gaji Buhari a zaben 2023

Yayin da ministan ke maida martani Ya ce,

“To, Kamata yai ace wadannan amsoshin tambayoyin da Atiku yayi, ya tambayi jam’iyyarsa, wacce a karkashin mulkinta aka fara Boko Haram a shekarar 2009 .
“Shekaru shidda, har zuwa 2015, lokacin da gwamnatinmu ta karbi mulki a hannunsu kuma muka gaji Boko Haram. Ya Kamata Atiku ya tambayi jam’iyyarsa dalilin da ya sa ta bar Boko Haram ta ta rinka gudanar da aiyukanta, da jefa bama-bamai a garuruwa, tashoshin moto, makarantu, da sauran wurare.

Ministan yada labaran ya kara da cewa a maimakon haka ya kamata dan takarar shugaban kasa ya godewa dakarun Nigeria sabida kishin kasa da zumar samar da zaman lafiya don bunkasar harkokin tattalin arzikin yanki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel