Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Wasu Mutum Biyu da Buhari Ya Nada a Mukamai
- Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar Buhari na naɗa mataimakan gwamnan babban bankin Najeriya CBN
- Idan baku manta ba ana ta kai ruwa rana kan batun sabon tsarin kayyade yawan kuɗin da mutum zai cire daga Asusu duk mako
- An yi tsammanin Sanatocin zasu titsiye mataimakan gwamnan yayin tantance su amma bisa mamaki hakan ba ta faru ba
Abuja - A ranar Laraban nan Majalisar Dattawa ta tabbatar da tsohon Darakta a Babban bankin Najeriya, Edward Lametek Adamu, a matsayin mataimakin gwamnan CBN domin ƙara shafe zango ɗaya a Ofis.
Majalisar ta kuma amince da sabunta naɗin mataimakiyar gwamnan CBN, Misis Aisha Ndanusa Ahmad, wacce zata wuce zango na biyu kuma na ƙarshe a mukamin.
Amincewa da naɗin mutanen biyu da Sanatocin suka yi ya biyo bayan nazari kan rahoton da kwamitin Banki, Inshora da sauran hukumomin da suka shafi kuɗi ya gabatar a zauren.
Yan Najeriya Sun Samu Sabon Sumfurin Shugaba Buhari, Doguwa Ya Jaddada Wanda Ya Dace da Mulki a 2023
Shugaban kwamitin kuma sanatan Kaduna ta tsakiya, Malam Uba Sani, ne ya gabatar da rahoton a gaban abokan aikinsa a zamansu na yau Laraba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar The Nation tace Bayan gabatar da rahoton, majalisar ta amince da shawarain da ya ƙunsa wanda ya roki mambobin majalisar su amince da waɗanda shugaban kasa ya naɗa.
Baki ɗaya Sanatocin sun amince da naɗin mutanen biyiu a matsayin mataimakan Bankin CBN yayin da mataimakin shugaban majalisar, Sanata Omo-Agege ya nemi a kaɗa kuri'un murya a zauren.
A ranar Talata, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya tura sunayen Ahmad da Adamu ga majalisar domin tantancewa da kuma tabbatar da sabunta naɗa su a matsayin zango na karshe.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa an samu wannan ci gaban ne yayin da ake kace-nace kan sabon tsarin CBN na taƙaita yawan kuɗin cirewa a kowace rana.
Na Yi Iya Bakin Kokarina a Matsayin Shugaban Kasa, Buhari
A wani labarin kuma Shugaba Buhari yace ya yi iya bakin kokarinsa a tsawon shekarun da ya kwashe kan madafun iko
A birnin Washington DC na ƙasar Amurka, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace duk da yawan al'umma da faɗin ƙasa, gwamnatinsa ta taka muhimmiyar rawa.
Yace matasa sune ƙashin bayan al'umma domin su ne shugabannin gobe bisa haka gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen inganta rayuwarsu.
Asali: Legit.ng