Dandalin Kannywood: Allah yayi wa fitaccen dan fim din Hausa, waragis rasuwa

Dandalin Kannywood: Allah yayi wa fitaccen dan fim din Hausa, waragis rasuwa

- Tabbas dukkan mai rai mamaci ne wata rana

- Allah ya yi wa Malam Muhammad Umar Waragis rasuwa da safiyar yau Talata

- Marigayin dai ya sha fama ne da matsananciyar jinya kafin rasuwar ta sa

Tabbas dukkan mai rai mamaci ne wata rana. Kamar dai yadda muka samu daga majiya mai tushe, fitaccen jarumin nan na masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakabi da Kannywood watau Malam Muhammad Umar Waragis ya rasa ransa da safiyar yau Talata 13 ga watan Maris, 2018.

Dandalin Kannywood: Allah yayi wa fitaccen dan fim din Hausa, waragis rasuwa
Dandalin Kannywood: Allah yayi wa fitaccen dan fim din Hausa, waragis rasuwa

KU KARANTA: Magu ya sake gano wasu makudan kudaden sata hannun wata makusanciyar Jonathan

Marigayin dai ya sha fama ne da matsananciyar jinya kafin rasuwar ta sa kamar dai yadda daya daga cikin 'ya'yan sa ya shaida mana.

Legit.ng dai a baya ta kawo maku labarin cewa Iyalan fitaccen dan fim din sun bayyana cewa suna cikin mawuyacin hali sakamakon rashin wadataccen kudin da za su ci gaba da jinyarsa a asibiti.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, an kwantar da Malam Waragis ne a wani asibiti dake garin Jos sakamakon ciwon koda da yake fama da ita.

Haka ma dai a yayin tattaki tun daga Kano domin duba lafiyar Malam Waragis da ya yi, fitaccen mawakin finafinan Hausa Sa'eed Nagudu ya baiwa iyalansa gudummawar kayan masarufi da kuma kudi, inda kuma ya yi fatan Allah ya tashi kafadun mara lafiyan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng