"Sun San Komai" Wata Malama Ta Fallasa Wasikar da Dalibanta Suka Aiko Mata, Mutane Sun Girgiza

"Sun San Komai" Wata Malama Ta Fallasa Wasikar da Dalibanta Suka Aiko Mata, Mutane Sun Girgiza

  • Wata Malama 'yar Najeriya ta wallafa Hotunan wasiƙa mai ratsa zuciya da ɗalibai suka aiko mata a aji
  • Yayin wallafa wasikun, budurwar wacce ta shiga yanayin farin ciki ta yaba wa ɗaliban tare da gaya musu cewa ta gamsu da koyarwar da take musu
  • Mutane sun yi rubdugun maida martani kan lamarin a Soshiyal midiya, wasu na ba da labarin soyayyar da suke wa malamansu

Wata Malama yar Najeriya mai suna Bridget Vincent ta taɓa zuciyoyin jama'a bayan ta wallafa wasu Hotunan wasiƙu da ta samu daga ɗaliban da take koyarwa.

A wasiƙun, ɗaliban malamar sun bayyana ƙaunar da suke mata kuma sun yi alƙawarin siya mata kyaututtuka ciki har da 'Chin Chin'.

Malamar Makaranta.
"Sun San Komai" Wata Malama Ta Fallasa Wasikar da Dalibanta Suka Aiko Mata, Mutane Sun Girgiza Hoto: Bridget Vincent
Asali: Facebook

Bridget, kyakkywa kuma dirarriyar mace tace ba ta taba sanin cewa ƙananan yaran na tasirantuwa da kokarin koyar da su da take ba har sai lokacin da ta karanta kalamansu.

Kara karanta wannan

So Ya Yi Dadi: Saurayin Online Ya Damafari Budurwa Miliyoyin Kudi, Labarin Ya Girgiza Mutane

Ta bayyana cewa duk da ba'a biyanta Albashi mai tsoka a makarantar, wasikun ɗalibanta kaɗai sun zarce kuɗin da ake biyanta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamanta, Bridget tace:

"Wannan ne sakon da na samu daga ɗalibaina, sun taɓa mun zuciyata, ban taba sanin sun gamsu da aiki na ba tsawon lokaci. Yadda wasu daga ciki suka rubuta sunana kaɗai ya ba ni nishaɗi."
"Kananan yara sun sane da komai, duk da ba ba'a biyan malamai Albashi mai kyau, wannan kaɗai ya biya ni, (farin ciki)."

Juke Karen ya ce:

"Wannan ya sa mutum ke bukatar ya yi takatsantsan wurin mu'amala da yara, suna gani da sanin komai dake faruwa a shekarunsu."

Dorca Owico tace:

"Ɗalibaina sun je siyo mun alewar ƙarin shekara kawai suka yi kicibus da wani ɗan siyasa suka roki ya siyamun Kek da ruwan roba a msatayin kyauta."

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Lokacin Da PDP Zata Yankewa Wike Da Ƴan G5 Hukunci

"Wannan abun da ya faru ya sa shagalin ya shiga zuciyata ban taɓa kamarsa ba. Kananan yaran nan cike suke da soyayya ina faɗa muku."

"Ya Hadu": Wata Budurwa Ta Bar Wani Saurayi Ya Kwanta a Jikinta, Hotonsu Ya Ja Hankali

A wani labarin kuma Wata Budurwa ta bayyana yadda ta ji a zuciya yayin da wani matashin Saurayi da suka haɗu a Mota ya kishingiɗa a jikinta

Da take ba da labari a wata wallafa a shafinta, kyakkyawar budurwar ta nuna yadda abun ya mata daɗi ganin mutumin ya ɗan huta a kafaɗarta.

Tace abun sha'awar shi ne duk da ya nuna alamun gajiya da zafin gari mutumin bai tambayeta kudi ba, tace ta yi dana sanin rashin karban lambarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel